From Wikipedia, the free encyclopedia
Claudine Gbènagnon Talon (an haife ta a shekara ta 1956) 'yar ƙasar Benin ce, 'yar siyasa, kuma uwargidan shugaban ƙasar Benin tun daga ranar 6 ga watan Afrilu 2016, a matsayin matar Patrice Talon, Shugaban Jamhuriyar Benin.
Claudine Talon | |||||
---|---|---|---|---|---|
2017 -
6 ga Afirilu, 2016 - | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Porto-Novo, 1957 (66/67 shekaru) | ||||
ƙasa | Benin | ||||
Ƴan uwa | |||||
Abokiyar zama | Patrice Talon | ||||
Yara | |||||
Karatu | |||||
Harsuna | Faransanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa |
An haifi Talon Claudine Gbenagnon a cikin shekarar 1956 a Porto-Novo.[1] Ta shiga siyasar Benin ta hannun mijinta, Patrice Talon, da kuma gidauniyarta. Bayan dogon rashi, Claudine Talon ta sake bayyana a bainar jama'a a ranar 26 ga watan Maris, 2021 jim kaɗan kafin zaɓen shugaban ƙasa.[2]
Bayan zaɓen mijinta a matsayin shugaban jamhuriyar Benin, ta kirkiro gidauniyar Claudine Talon. Manufar gidauniyar dai ita ce inganta rayuwar mata da yara 'yan ƙasar ta Benin, tare da kara samar da tsaftataccen ruwan sha da tsaftar muhalli ga al'ummar ƙasar. Har ila yau, yana da niyyar inganta ingantaccen ilimin yara da ƙarfafa mata marasa galihu.[3]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.