COVID-19 a Najeriya
From Wikipedia, the free encyclopedia
From Wikipedia, the free encyclopedia
Farkon samun bullar ibtala'in annobar cutar COVID-19 ko Koronavirus 2019 a Najeriya ya bulla ne a Jahar Lagos ranar 27 ga watan Fabrairu 2020, lokacin da wani dan kasar Italiya ya shiga kasar dauke da cutar.[1][2] A ranar 9 ga watan Maris shekara ta 2020, aka samu labarin bullar annobar a karo na biyu a kasar ta Najeriya a Jahar Ogun, Inda aka samu wani dan Najeriya wanda yayi mu'amala da dan kasar Italiya mai dauke da cutar shima ya kamu.[3]
| ||||
| ||||
Iri | Annoba de Koronavirus 2019 | |||
---|---|---|---|---|
Bangare na | COVID-19 pandemic a Africa da COVID-19 pandemic by country and territory (en) | |||
Kwanan watan | 27 ga Faburairu, 2020 – | |||
Wuri | Najeriya | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Sanadi | Koronavirus 2019 | |||
Hashtag (en) | #CoronaVirusNigeria | |||
A ranar 28 ga watan Janairu shekara ta 2020, ne Najeriya ta aiyana tsagaita zirga-zirga a wasu filayen jirgin sama na kasar duka dai domin ganin an dakile yaduwar annobar ta COVID-19 a fadin kasar. Tashoshin Jiragen saman Kano, Inugu, Lagos, Ribas da Babban birnin taraiya ne gwamnagin ta sanar da rufe su.[4] Hukumar dake kula da yaduwar annoba ta kasar ta sanar da shirinta na tunkarar annobar COVID-19 a kasar.[5]
A ranar 31 ga watan Janairu shekara ta 2020 ne gwamnatin ta shirya rukuni na masana domin shirya yadda za'a dakile bazuwar cutar a kasar. Hakan kuwa nazuwa ne tuntun bayan ganin yadda annobar ta COVID-19 ke kara mamaye birane ka kasar Sin.[6][7] A wannan ranar dai Hukumar lafiya ta duniya ta lisafta Najeriya cikin jerin kasashen Afrika 13 da ibtala'in ka iya afkawa.[8]
A ranar 26 ga watan Fabarairu shekara ta 2020, wani dan kasar Sin ya kai kansa wajen gwamnatin jihar Lagos domin ta dubashi koda yana dauke da cutar, inda aka kaishi asibitin Reddington kuma aka sallame shi bayan kwana daya, bayan sakamakon gwaji ya tabbatar baya dauke da cutar.[9]
Ranar 27 ga watan Fabrairu shekara ta 2020 aka samu bullar cutar karon farko a Najeriya, lokacin da wani dan kasar Italiya ya baro birnin Milan ya sauka a filin jirgin sama na Murtala Muhammed, dake Lagos.[10][11][12][13][14]
A ranar 9 gaga watan garin shekara ta 2020, aka samu bayanin bullar annobar karo na biyu a garin Ewekoro na Jahar Ogun, wanda shima yayi huldahulda da dankasar Italiya mai dauke da cutar.[15][16][17]
A ranar 13 ga watan Mari shekara ta 2020, ne Najeriya ta fitar da sanarwar wanda aka samu na biyu dauke da cutar bashi da ita bayan anyi masa gwaje gwaje.[18]
Ranar 17 ga watan Maris shekara ta 2020, gwamnatin jihar Lagos ta fitar da rahoton tabbacin samun mutum na uku dauke da cutar. Wata mata ce yar shekara 30 wadda ta dawo daga kasar Birtaniya.[19]
Ranar 18 ga watan Maris shekara ta 2020, Najeriya ta kara tabbatar da samun Karin mutum biyar dauke da cutar.
Ranar 23 ga watan Maris, shekara ta 2020 ne Hukumar da ke hana yaduwar cutuka ta Najeriya NCDC ta ce mutum daya daga cikin mutum 35 da suka kamu da cutar Coronavirus ya mutu. A shafinta na Twitter, hukumar ta ce mutumin mai shekara 67 ya koma Najeriya daga kasar Burtaniya. NCDC ta kara da cewa da ma marigayin yana fama da cutar suga da daji inda ake yi masa gashi a asibiti.[20]
An fara gano cutar korona a Najeriya ne a jikin wani baturen kasar Italiya ranar 27 ga watan Fabrairu bayan ya shiga kasar ta filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas. Shi da mutum na farko da ya kamu da cutar ranar 20 ga watan Maris a arewacin Najeriya, Mohammed Atiku duk sun warke kuma an sallame su daga asibiti. A ranar Juma'a 17 ga watan Afrilu ne cutar korona ta yi sanadin mutuwar Malam Abba Kyari, shugaban ma'aikatan fadar shugaban Najeriya. Shi ne mutum mafi girman mukami da ya mutu dalilin korona a kasar. Gwamnoni irinsu Bala Mohammed da Nasir El-rufa'i da kuma Seyi Makinde na jihar Oyo duk sun kamu da annobar kafin su warke daga bisani. Har yazuwa ranar Alhamis 27 ga watan Mayu shekara ta 2020, a hukumance ba a samu bullar cutar a jihohin Kogi da Cross river ba, amma wasu na da ra'ayin cewa hakan ta faru ne saboda ba a gwajin cutar a cikin johohin biyu. Hukumomin Najeriya dai sun ce sun rubanya adadin gwaje-gwajen da suke yi a kasar, inda a yanzu suka ce akan yi gwaji kimanin dubu guda cikin sa'a 24.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.