From Wikipedia, the free encyclopedia
Manjo Janar Abdullahi Sarki Mukhtar (Rtd) (An haife shi ranar 5 ga Yuli, 1949) a Jihar Kano. Ya taba zama mai baiwa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro. Rtd Manjo Janar Mukhtar ya kuma kasance tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna da jihar Katsina, idan aka yi la’akari da shi ne shugaba ko gwamna na farko.[1]
Abdullahi Sarki Mukhtar | |||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|
ga Yuli, 1988 - ga Augusta, 1990 ← Dangiwa Umar - Abubakar Tanko Ayuba →
Satumba 1987 - ga Yuli, 1988 - Lawrence Onoja →
| |||||||
Rayuwa | |||||||
Haihuwa | jihar Kano, 5 ga Yuli, 1949 (75 shekaru) | ||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||
Harshen uwa | Hausa | ||||||
Karatu | |||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||
Sana'a | |||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||
Digiri | Janar |
Ya yi fice sosai a aikin soja har zuwa lokacin da aka nada shi babban hafsan kwamandan runduna ta farko, sojojin Najeriya a Jihar Kaduna, kafin wannan lokacin ya kasance shugaban ma’aikatan rundunar wanzar da zaman lafiya a kasar Laberiya. Mukhtar na daya daga cikin manyan hafsoshin najeriya.[2]
An san shi a matsayin jami’i mai ka’ida kuma mai kwarjini wanda ya samu karramawar shugaba Obasanjo a lokacin da ya ki amincewa da bukatar Sani Abacha kan yadda aka yi wa wadanda ake zargi da juyin mulki a shekarar 1995.[3] Daga ranar 23 ga Janairu, 2002, zuwa 30 ga Mayu, 2003, ya Gudanar da Ofishin Jakadancin Najeriya a Moscow.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.