Birni a Arewa na Ghana. From Wikipedia, the free encyclopedia
Tamale birni ne mai saurin cigaba a Yammacin Afrika. Shine babban birnin arewacin kasar Ghana. Birnin cibiya ce ta kasuwanci a yankin. Waje ne mai kwanciyar hankali sannan kuma mai sauki wajen kasuwanci. Mutanen birnin mutane ne masu son zaman lafiya. Tamale shine birni na uku mafi girma a kasar Ghana. Yana da yawan jam'a kimanin 950,124 kamar yadda shafin yanar gizo mallakin birnin ya ruwaito. Shine birni mafi saurin cigaba a Yammacin Afrika.[1][2] Birnin na a 600 km (370 mi) north of Accra.[3]
Tamale, Ghana | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Ghana | |||
Yankuna na Ghana | Yankin Arewaci | |||
Gundumomin Ghana | Tamale Metropolitan District | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 466,723 (2016) | |||
• Yawan mutane | 622.3 mazaunan/km² | |||
Harshen gwamnati |
Turanci Harshen Dagbani | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 750 km² | |||
Altitude (en) | 151 m | |||
Sun raba iyaka da | ||||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
UTC±00:00 (en)
| |||
Wasu abun | ||||
| ||||
Yanar gizo | tamale.ghanadistricts.gov.gh |
Mafi akasarin mazauna birnin Tamale Musulmai ne, akwai Masallatai da dama a Tamale, mafiya shahara sune, Masallacin Afa Ajura (masallacin Ambariyyah), da kuma masallatan kungiyar da'awa ta Ahmadiyya.
Tamale na a Arewacin Ghana ne, asalinta daga masarautar Dagbon ta fita. Sarkin shine sarkin al'umar Dagomba wato sarkin Yendi.
Sakamakon kasantuwar Tamale a tsakiya ne yasa birnin yazama matatara ta gudanarwar gwamnati da cibiyar kasuwanci da siyasa a arewacin Ghana.[4]
Cigaban Tamale yazo ne cikin shekaru kadan da suka gabata .[5]
Tsarin Gwamnatin Tamale na tafiya ne karkashin ofishin magajin gari wanda shugaban kasar Ghana ne keda ikon nada shi. Magajin garin T Tamale na yanzu shine Hon. Iddrisu Musah. Akwai majalisa mai dauke da wakilai yan majalisu masu gudanarwa.
Tamale nada muhimmancin gaske a fannin ilimi a kasar Ghana. Ya zuwa yanzu, akwai makarantu 742 a tsakiyar birnin. Wannan ya hada da makarantun Nazire guda 94, Firamare 304, kananan sakandare 112 da kuma manyan sakandare 14. Sauran sun hada da makarantu na koyo a aikace, sai kwalejin ilimi biyu, jami'ar fasaha da wasu jami'oi biyu masu zaman kansu.[5]
Tamale nada muhimmancin gaske a fannin sufuri a kasar Ghana. Akwai Filin jirgin saman Tamale..[6]
Akwai motocin haya na tasi, da babura masu kafa uku wadanda ake kira da "Mahama-Cambuu". Su Mahama Cambuu sunane da aka lakabawa babura masu kafa uku ma'ana " Mahama zai yi". Mahama din shine tsohon shugaban kasar Ghana, H.E John Dramani Mahama. Suna da sauki ba kamar tasi ba, kuma zasu kaika dukan lungun da zaka. Akwai kuma babura masu kafa biyu wadanda akafi sani da yan acaba.
Hotunan wasu sassa daga birnin Tamale.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.