Sinima na Ukrainian ya ƙunshi fina-finai na fasahar da shirye-shirye na kirkira wadanda aka shirin a cikin kasar Ukraine ko kuma masu shirya fina-finai na Ukrain a kasashen ketare.
Duk da tarihin muhimmanci da kuma kayatattun shirye-shiyensu, akwai jayayya da dama aka matsayin kafar shirye-shiryen, dangane da tasirin Russia da Kasashen turai ga sinimar.[1] Furodusoshin sinimar Ukraine na ayyuka na hadin gwiwa a kasashe daban daban, yayin da darektoci, jarumai da kuma ma'aikatan shiri na fitowa a fina-finan Russia (Soviet Union a da). Fina-finan da suka samu karbuwa sun kasance game da mutanen kasar Ukraine ne, labaransu ko kuma wami al'amari da ya faru, kamar su Battleship Potemkin, Man with a Movie Camera, da kuma fim din Everything Is Illuminated.
Ma'aikatar shirya fina-finai ta Ukraine wato Ukrainian State Film Agency ke da alhakin kula da cibiyar National Oleksandr Dovzhenko Film Centre, fannin kula da kwafan fina-finai da kuma tattara su. Wani bikin fina-finai da ake kira Molodist wanda ake yi a birnin Kyiv shi kadai ne biki na ƙasa da ƙasa da aka yarje mawa wanda ake gudanarwa a kasar Ukraine, sashin gasar ya hada da sashin fina-finan dalibai, gajerun fina-finai na farko-farko, da kuma fina-finan hadin gwiwa na sassa daban daban na duniya. Ana gudanar da bikin ne a watan Oktoba na kowacce shekara.
Kasar Ukraine tana da tasiri matuka ga sinimar ta Ukraine. Shahararrun daraktocin Ukraine sun hada da Oleksandr Dovzhenko, Dziga Vertov da Serhiy Paradzhanov. Ana kuma ambatan Dovzhenko sau da yawa a matsayin ɗaya daga cikin mafi mahimmancin masu shirya fina-finai na lokacin yankin Soviet da ya gabata, da kuma kasancewa majagaban shirin Soviet montage theory da kafa Dovzhenko Film Studios, sai kuma SergeiParadzhanov wani darektan fina-finai na kasar Armeniya kuma mawaki wanda ya ba da gudummawa da dama ga sinimar kasar Ukraine, da ta Armeniya da kuma sinimar kasar Georgia. Ya kuma ƙirƙiri nasa salon sinimar, wakokin sinimar ta Ukrainian, wanda sun sha bambam da gundarin ka'idodin gurguzanci na kasar.
Yawancin 'yan wasan kwaikwayo na asalin Ukrainian sun sami shahara a duniya da nasara masu tasiri matuka, ciki har da Vira Kholodna, Bohdan Stupka, Sergei Makovetsky, Mike Mazurki, Natalie Wood, Danny Kaye, Jack Palance, Milla Jovovich, Olga Kurylenko da Mila Kunis.
A cikin yankin Odesa film studio, akwai wurin kayan tarihi na "Museum of the Cinema", inda za'a iya gani ababan sha'awa daban daban dangane da wannan sinimar na baki daya ko kuma tarihin sinimar ta Ukraine ita kadai. Anan za a iya samun kayan tarihi, na daga ƙirƙira na sinimar, zuwa zamani, dijital da avant garde.
Fina-finan kasar Ukraine SSR ta hanyar siyar da tikitai
Ma'aikatar Al'adu ta Ukraine da Ƙungiyar Cinematographers na Ukrainian ke gudanar da wannan sashin.
Cibiyar zartarwa na shirye-shiryen sinima a Ukraine ita ce Hukumar Kula da Fina-Fina ta Ukrainian (USFA). Tare da Gidauniyar Al'adu ta kasar Ukraine, wacce ita ce tafi kowa sanya hannun jari a sinimar ta Ukraine kuma yi zuwa shekara ta 2019 kowane daga cikin waɗannan cibiyoyin na sanya hannun jari kusan miliyan UAH 500 a wurin samar da fina-finai a Ukraine.
Kamfanin Rarraba Fim na B & H shine babban mai rarraba fina-finan kasar Ukraine; kuma su ke watsa fina-finan kasar ta Walt Disney Pictures, Universal Pictures, Paramount Pictures, Sony Pictures Entertainment (Columbia Pictures).
Na'aiktar Rarraba Fim na Ukraine (wanda akafi sani da Gemini Ukraine) su ke da alhakin rarraba fina-finai na gida ta kafar 20th Century Fox (Fox Searchlight Pictures, Blue Sky Studios).
VLG FIM (wanda akafi sani a da da Volga Ukraine) shi ke da alhakin rarraba fina-finai na gida ta Miramax, StudioCanal, STX Entertainment, A24, Lionsgate, Focus Features International, EuropaCorp, Pathé Exchange, Kinology, Affinity Equity Partners, Exclusive Media Group, TF1 da sauransu.
Kinomania shine mai rarraba fina-finai na gida na Warner Brothers (New Line Cinema).
Gajerun fina-finai, wanda sukayi nasara a bukukuwa da gidajen fasaha galibi ana rarraba su ta hanyar kafar Arthouse [4]
Molodist, Kyiv International Film Festival, wanda aka gudanar a Kyiv (1970-)
Kyiv International Film Festival (KIFF), da aka gudanar a Kyiv (2009-)
Kyiv International Short Film Festival (KISFF), [5] da aka gudanar a Kyiv (2012-)
Kinolev, wanda aka gudanar a Lviv (2006-)
Odessa International Film Festival, [6] da aka gudanar a Odesa (2010-)
Animation Film Festival "Krok", (1987) shirya ta Ukrainian Association of Cinematographers da kuma faruwa a Ukraine da kuma Rasha .
Pokrov, bikin kasa da kasa na cinema na Kiristanci na Orthodox, wanda aka gudanar a Kyiv (2003-)
Vidkryta Nich (Open Night), bikin na farkon fina-finai na Ukrainian, wanda aka gudanar a Kyiv (1997-)
Kharkiv Siren Film Festival, bikin kasa da kasa na gajerun fina-finai, wanda aka gudanar a Kharkiv (2008-)
Wiz-Art, International Short Film Festival, wanda aka gudanar a Lviv (2008-)
VAU-Fest, International Video Art and Short Film Festival, wanda aka gudanar a garin Ukrainka a yankin Kyiv (2010-)
Kinofront, bikin Ukrainian Z da fina-finan indie (2008-)
Docudays UA, bikin shirya fim na haƙƙin ɗan adam na duniya, wanda aka gudanar a Kyiv tare da shirin balaguro a kusa da Ukraine (2003-)
Tuntuɓi, bikin fina-finai na shirin kasa da kasa, wanda aka gudanar a Kyiv (2005-2007)
Berdiansk International Film Festival "Golden Brigantine", bikin cinema da aka yi a Commonwealth of Independent States and Baltic countries, wanda aka gudanar a birnin Berdiansk (2011)
Irpin Film Festival, bikin kasa da kasa na madadin cinema, wanda aka gudanar a garin Irpin (2003)
Golden Pektorale, International Truskavets Film Festival, wanda aka gudanar a garin Truskavets
Crown of Carpathians, [7] Wani Bikin Fim na Truskavets na Duniya, wanda aka gudanar a garin Truskavets
Mute Nights, Odesa, International shiru film Festival wanda aka gudanar a Odesa a kan mako na uku a kan Yuni.
Kino-Yalta, bikin fina-finan furodusa (2003) da aka shirya tare da gwamnatin Rasha.
Sebastopol International Film Festival, da aka gudanar a Sevastopol, Crimea (2005-2009, 2011)
Kyaututtuka na yanzu
Shevchenko National Prize, don shirya Fasaha
Dovzhenko State Prize na Ukraine
Barewa na Scythian, babbar kyauta na Molodist Festival na Student Cinematography Festival
Golden Dzyga (Ukrainian Film Academy Awards), babban kyautar Odessa International Film Festival (OIFF) [9]
Sunny bunny na bikin fim ɗin ɗalibi na ƙasa da ƙasa Molodist
Ukrainian Panorama na kasa da kasa dalibi cinematography bikin Molodist
A cikin shekara ta 1987, injiniyan kasar Ukraine kuma mai kirkira Eugene Mamut tare da abokan aikinsa su uku sun sami lambar yabo ta Oscar ( Kyautar Kimiyya da Injiniyanci ) don ƙira da haɓaka RGA / Oxberry Compu-Quad Special Effects Optical Printer don fim ɗin Predator.
A cikin shekara ta 2006, injiniyan Ukrainian kuma mai ƙirƙira Anatoliy Kokush ya sami lambar yabo ta Oscars biyu don dabaru da haɓaka kyamarori na Ukrainian gyro-stabilized crane da Kan jirgi.
Tsofaffin kyaututtuka
Lenin Komsomol Prize na Ukrainian SSR
1910 Шемелько-денщик або Хохол наплутав / Shemelko-Denshchyk, directed by Oleksandr Ostroukhov-Arbo
1912 Запорізька січ / Zaporizhian Sich, directed by Danylo Sakhnenko
1912 Любов Андрія / Andriy's Love, directed by Danylo Sakhnenko
1913 Полтава / Poltava, directed by Danylo Sakhnenko
Rubutun fina-finai a harshen Ukraine yana nufin rubutun shirye-shiryen samfuran bidiyo (fina-finai, jerin wasannin talabijin, wasannin bidiyo, da sauransu) a cikin harshen kasar Ukraine.
A shekara ta 2010, kashi ɗaya bisa uku na daukakin fina-finan kasar Ukraine an yi su ne da harshen Rashanci.[11] A cikin 2019, Majalisar Dokokin Yukren ta zartar da wata doka da ke ba da tabbacin cewa duk fina-finai suna yin murguda ko juzu'i a cikin yaren Ukrainian. A cikin 2021, Netflix sun fitar da fim ɗin fasalin su na farko tare da bugar Ukrainian. Kashi 11% na ƴan ƙasar Ukrain ne kaɗai ke adawa da buga fim ɗin.
'Yan wasan kwaikwayo a harshen Ukraine
Tun da kafuwar kwaikwayo na murya a harshen kasar Ukraine a 2006, akwai mutane da yawa da ake yawan jin muryoyinsu a cikin wasannin kwaikwayo na
Ukraine, daga cikin mafi shaharar su akwai Eugene Maluha (wanda akafi sani da Ukrainian Alfa voice daga cikin jerin fina-finan "cult series") da kuma Yuri Kovalenko (wanda aka sani da Ukrainian cheesecakes voice). a cikin fim din Cars - na fim mai cikakken tsawo na shahararren fim na zane wato (animation), wanda aka nuna a sinimar Ukraine tare da muryoyin 'yan wasan kasar Ukraine).
Taurarin wasan kwaikwayo na kasar Ukraine suma suna da hannu sosai wajen yin muryoyi a cikin fina-finan harshen Ukraine. Yawancin mashahuran mawaƙa, ciki har da Oleg Skrypka da Ani Lorak, sun shiga cikin buga fim na zane wato Carlson, wanda aka shirya a shekara ta (2002). Yawancin mashahurai sun yi aiki a shirin cartoon naTerkel da Khalepa (2004): Potap, Oleg Skrypka, Fagot da Fozzy (TNMK band), Foma ( Mandry band ), Vadim Krasnooky ( Mad Heads band ), Katya Chilly, Vitaliy Kozlovsky, Lilu, Vasya Gontarsky ( "Vasya Club"), DJ Romeo dan Stepan Kazanin (Quarter-95). A cikin shirin cartoon na Horton (2008) za ku iya jin muryoyin masu jarumai kaman Pavel Shilko (DJ Pasha) da Vladimir Zelensky (Quarter-95). Muhimman jarumai a fim din "13th District: Ultimatum" (2009) a cikin akwatin shirye-shiryen Ukrain anyi magana da muryoyin Yevhen Koshov ( Quarter-95 ) da kuma Andriy Khlyvnyuk (soloist na kungiyar " Boombox ").
'Yan wasan kwaikwayon kasar Ukraine
Bohdan Kozak (Nuwamba 27, 1940)
Ivan Mykolaichuk (15 ga Yuni, 1941 - Agusta 3, 1987)
Bohdan Stupka (Agusta 27, 1941 - Yuli 22, 2012)
Rayisa Nedashkivska (Fabrairu 17, 1943)
Mykhailo Holubovych (Nuwamba 27, 1940)
Ivan Havryliuk (Oktoba 25, 1948)
Serhiy Romaniuk (Yuli 21, 1953)
Bohdan Beniuk (Mayu 26, 1957)
Ruslana Pysanka (Nuwamba 17, 1965)
Taisia Povaliy (10 ga Disamba, 1965)
'Yan wasan kwaikwayo Ukrain na waje
Vira Kholodna (1893-1919)
Gregory Hlady (Disamba 4, 1954)
David Vadim (Maris 28, 1972)
Eugene Hütz (Satumba 6, 1972)
Oleg Prudius (Afrilu 27, 1972)
Vera Farmiga (Agusta 6, 1973)
Milla Jovovich (17 ga Disamba, 1975)
Katheryn Winnick (17 ga Disamba, 1977)
Olga Kurylenko (Nuwamba 14, 1979)
Mila Kunis (Agusta 14, 1983)
Baƙi daga Ukraine sun kasance iyaye ko kakanni na Serge Gainsbourg, Leonard Nimoy, Vira Farmiga, Taissa Farmiga, Steven Spielberg, Dustin Hoffman, Sylvester Stallone, Kirk Douglas, Leonardo DiCaprio, Winona Ryder, Whoopi Goldberg, Edward Zonny Krakz, Edward Dmy Krakz, da Edward Dmy Krakz ., mai rugujewa David Copperfield, mai wasan kwaikwayo Bill Tytla.
Darektocin Ukraine
Oleksandr Dovzhenko ( September 10 [ - Nuwamba 25, 1956)
Viktor Ivchenko (Nuwamba 4, 1912 - Nuwamba 6, 1972)
Mykola Mashchenko (Janairu 2, 1929 - Mayu 2, 2013)
Vadym Illienko (Yuli 3, 1932 - Mayu 8, 2015)
Yuriy Illienko (16 ga Yuli, 1936 - Yuni 15, 2010)
Leonid Osyka (Maris 8, 1940 - Satumba 16, 2001)
Mykhailo Illienko (29 ga Yuni, 1947)
Andriy Donchyk (11 ga Satumba, 1961)
Igor Podolchak (Afrilu 9, 1962)
Myroslav Slaboshpytskyi (17 ga Oktoba, 1974)
Vyacheslav Krishtofovich
Sergiy Masloboyschikov
Maryna Vroda
Daraktoci waɗanda ba 'yan asalin kasar Ukrainian ba
Dziga Vertov (2 Janairu 1896 - 12 Fabrairu 1954)
Anatole Litvak (Mayu 10, 1902 - Disamba 15, 1974)
Sergei Bondarchuk (25 ga Satumba, 1920 - Oktoba 20, 1994)
Grigori Chukhrai (Mayu 23, 1921 - Oktoba 28, 2001)
Sergei Parajanov (Janairu 9, 1924 - Yuli 20, 1990)
Leonid Bykov (12 ga Disamba, 1928 - Afrilu 11, 1979)
Shevchuk, Yuri (2014). Linguistic Strategies of Imperial Appropriation: Why Ukraine is absent from world film history. Ch. 22 of Contemporary Ukraine on the Cultural Map of Europe, ed. Larissa M. L. Zaleska Onyshkevych & Maria G. Rewakowicz. Routledge. pp. 359–374. ISBN9781317473787.
"Сьогодні кожний третій фільм йде російською. Азаров вимагає негайно покінчити з україномовним дубляжем". Українська правда - Блоги. Retrieved 2021-02-28.