![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/8e/Sanusi_Lamido_Sanusi_01.png/640px-Sanusi_Lamido_Sanusi_01.png&w=640&q=50)
Sanusi Lamido Sanusi
From Wikipedia, the free encyclopedia
Sanusi Lamido SanusiSanusi Lamido Sanusi (Taimako·bayani) (An haife shi a ranar 31 ga watan Yuni, alif ɗari tara da sittin da ɗaya shekara ta (1961)[1] miladiyya Isa dan Maryam. Ɗan gidan sarautan Kano ne kuma tsohon Shugaban babban bankin Nijeriya (CBN)[2]. A yanzun sarkin Kano na 14 da Kuma na 15. An naɗa shi sarauta ne a ranar takwas ga watan Yuni na shekara ta dubu biyu da goma sha huɗu, 2014 bayan rasuwar tsohon sarkin Kano Ado Bayero.[3] Zuwa 9 ga watan march shekara ta dubu biyu da ashirin, 2020. Sarki Sanusi ma'aikacin banki ne, wanda shine tsohon Shugaban Babban Bankin Nijeriya[4]. Wanda ya riƙe muƙamin tun daga uku (3) ga watan Yuni na shekara ta dubu biyu da tara, 2009, da yayi tsawon shekara biyar akai, kamar yadda dokar mukamin ya tabbatar amma sai dai Sanusin bai cika shekarunsa ba inda tsohon shugaban ƙasa na waccan lokaci, wato Goodluck Jonathan[5] ya tsige shi a ranar ashirin ga watan February shekara ta dubu biyu da goma sha huɗu, 2014, sanadiyar Sanusi ya bankaɗo wani zargi na badaƙalar kuɗi $20 billion a hukumar matatar man fetur na ƙasa (NNPC).
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/1/15/Sanusi_Lamido_Sanusi_World_Economic_Forum_2013.jpg/640px-Sanusi_Lamido_Sanusi_World_Economic_Forum_2013.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/e/e9/Emir_of_Kano.jpg/640px-Emir_of_Kano.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/8e/Sanusi_Lamido_Sanusi_01.png/320px-Sanusi_Lamido_Sanusi_01.png)
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||
8 ga Yuni, 2014 - ← Ado Bayero
3 ga Yuni, 2009 - 20 ga Faburairu, 2014 | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Kano, 31 ga Yuli, 1961 (62 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
Jami'ar Ahmadu Bello King's College, Lagos | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | Ma'aikacin banki da Malami | ||||
Mahalarcin
| |||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/c/c9/Emir_Muhammad_Sanusi_II_with_US_Special_Rep_to_Muslim_Communites%2C_Shaarik_H_Zafar_2.jpg/640px-Emir_Muhammad_Sanusi_II_with_US_Special_Rep_to_Muslim_Communites%2C_Shaarik_H_Zafar_2.jpg)
Sanusi jika ne na Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I, Sarki na 11th cikin sarakunan Fulani Na Kano.[6] Ma'aikacin banki ne kuma babban mutum ne, Malamin addinin musulunci ne da ake girmamawa.[7] Tun bayan sauƙe sarkin Kano Sanusi na II da gwamnatin jahar ta yi daga sarautar Kano, inda ya koma jihar Legas da zama, tsohon sarkin ya kai ziyarar sa ta farko a jihar Kaduna a ranar 23 Augusta 2020. Inda yazo dan girmama aikin da gwamnan jihar Malam Nasiru El-Rufai[8] ya bashi tun bayan sauke shi daga kujerarsa.[9]
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/f/f2/Image_of_Emir_Muhammad_Sanusi_II_of_Kano.jpg/640px-Image_of_Emir_Muhammad_Sanusi_II_of_Kano.jpg)