Pablo Picasso
From Wikipedia, the free encyclopedia
Pablo Picasso mai fenti ne. Picasso an haife shi a Malaga (yanzu Hispania) a shekara ta 1881, ya mutu a Mougins (Faransa) a shekara ta 1973. Ya kasance mai zane dan kasar Sipaniya, mai sassake-sassake, masanin gidan wasan kwaikwayo wanda ya kwashe mafi yawan rayuwarsa a kasar Faransa. Ya kasance daya daga cikin masu zane da suka shahara a ƙarni na 20. Yayi fice na musamman ta salon zanensa da ya kirkiri na “Cubism”, salon “constructed sculpture”, da kuma salon zane na “Collage”,[1][2] da dai sauran salon zane da ya taimaka wajen bunkasawa. Daga cikin fitattun ayyukansa akwai Zanen Proto-Cubism, Zanen Les Demoiselles d'Avignon, da zanen anti-war da dai sauransu.
Pablo Picasso | |||
---|---|---|---|
Murya | |||
| |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Pablo Diego José Francisco de Paula Juan Nepomuceno María de los Remedios Cipriano de la Santísima Trinidad Ruiz y Picasso | ||
Haihuwa | Malaga, 25 Oktoba 1881 | ||
ƙasa | Ispaniya | ||
Mazauni |
Château of Vauvenarg (en) Mas Notre-Dame-de-Vie de Mougins (en) rue des Grands-Augustins (en) | ||
Ƙabila | Spaniards (en) | ||
Harshen uwa | Yaren Sifen | ||
Mutuwa | Mas Notre-Dame-de-Vie de Mougins (en) da Mougins, 8 ga Afirilu, 1973 | ||
Makwanci | Château of Vauvenarg (en) | ||
Yanayin mutuwa |
Sababi na ainihi (pulmonary edema (en) Gazawar zuciya) | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | José Ruiz y Blanco | ||
Mahaifiya | Maria Picasso | ||
Abokiyar zama |
Olha Khokhlova (en) (12 ga Yuli, 1918 - 11 ga Faburairu, 1955) Jacqueline Roque (en) (2 ga Maris, 1961 - 8 ga Afirilu, 1973) | ||
Ma'aurata |
Nusch Éluard (en) Dora Maar (en) Fernande Olivier (en) Marie-Thérèse Walter (en) Françoise Gilot (en) Eva Gouel (en) | ||
Yara | |||
Ahali | Lola Ruiz Picasso (en) | ||
Ƴan uwa |
view
| ||
Karatu | |||
Makaranta |
Escola de Arte e Superior de Deseño Pablo Picasso (en) Royal Academy of Fine Arts of San Fernando (en) (1897 - | ||
Harsuna |
Catalan (en) Faransanci Yaren Sifen | ||
Malamai |
José Ruiz y Blanco (en) Isidoro Brocos (en) Antonio Muñoz Degrain (en) | ||
Ɗalibai | |||
Sana'a | |||
Sana'a | painter (en) , Mai sassakawa, mai zanen hoto, printmaker (en) , Mai tsara rayeraye, ceramicist (en) , poster artist (en) , illustrator (en) , mai daukar hoto, Mai zana kaya, designer (en) , jewelry designer (en) , mai zane-zanen hoto, architectural draftsperson (en) , muralist (en) , assemblage artist (en) , collagist (en) , mai tsara bangarorin fim, drawer (en) , marubin wasannin kwaykwayo da mai zane-zane | ||
Mahalarcin
| |||
Wurin aiki | Faris, Royan (en) , Aix-en-Provence (en) , Avignon, Antibes (en) , Schoorl (en) , A Coruña (en) , Barcelona da Madrid | ||
Muhimman ayyuka |
Guernica (en) Les Demoiselles d'Avignon (en) Chicago Picasso (en) Three Musicians (en) Science and Charity (en) Garçon à la pipe (en) Massacre in Korea (en) | ||
Kyaututtuka |
gani
| ||
Wanda ya ja hankalinsa | Henri Rousseau (en) , Paul Cézanne (en) , Sassaka a Africa da Maria Prymachenko (en) | ||
Mamba |
Academy of Arts of the GDR (en) Accademia delle Arti del Disegno (en) | ||
Fafutuka |
Cubism (en) surrealism (en) post-impressionism (en) | ||
Sunan mahaifi | Pau de Gósol | ||
Artistic movement |
painter (en) Mai sassakawa art of sculpture (en) graphics (en) ceramic (en) designer (en) figurative art (en) self-portrait (en) Hoto (Portrait) nude (en) figure (en) history painting (en) mythological painting (en) allegory (en) animal art (en) abstract art (en) landscape painting (en) marine art (en) still life (en) vanitas (en) | ||
Imani | |||
Addini |
mulhidanci lapsed Catholic (en) | ||
Jam'iyar siyasa | French Communist Party (en) | ||
IMDb | nm0681444 | ||
Picasso ya nuna bajinta da kwarewa a harkokin zane da dama a lokacin kuruciyarsa, inda yake zane acikin salo na musamman tun yana ƙarami har zuwa tsufansa. A farkon shekaru goma na karni na 20, salonsa sun canza yayinda ya ƙirƙiri kuma ya gwada sabbin dabaru da salo. Bayan shekarun 1906, dabarun tsohon mai zane Henri Matisse sun karawa Picasso karfin gwiwa sake nemo sabbin dabaru, wanda hakan ya janyo adawa a tsakanin masu zanen guda biyu, wadanda masu binciken zane suke alakantasu a matsayin jagororin masu zane na zamani.[3][4][5][6]
An rarraba ayyukan Pissaco zuwa lokuta daban daban. Yayinda har yanzu ana jayayya akan sunayen mafi akasarin ayyukansa. Lokutan ayyukansa da suka fi fice sune kamar haka: Lokacin Bula na Picasso (1901–1904), Lokacin Rose Picasso (1904–1906), Lokacin Zanen Afurkawa (1907–1909), Analytic Cubism (1909–1912), da kuma Synthetic Cubism (1912–1919) wanda kuma ake kira da Crystal Cubism. Mafi akasarin ayyukan Picasso a tsakanin shekarun 1910s da farkon shekarun 1920s sun kasance acikin salo irin na neoclassical sannan ayyukansa a tsakiyan shekarun 1920s suna da alaka da Surrealism. Ayyukansa na baya-baya suna da alaka da salonsa na tun yana karami.
Ya samar da zane da dama na musamman a daukakin rayuwarsa, Picasso ya samu shahara a duniya kuma ya tara dukiya mai yawa a dalilin nasarorinsa a zane kuma ya zamo daya daga cikin masu zane na musamman na ƙarni na 20.