Sarkin Bichi From Wikipedia, the free encyclopedia
Nasiru Ado BayeroNasiru Ado Bayero (Taimako·bayani) (An haife shi ne a ranar 2 ga watan Fabrairu na shekara ta alif ɗari tara da sittin da huɗu (1964) Miladiyya (A.c). kuma shi ne sarki na (2 )na Bichi . Ya hau gadon sarautar ne daga hannun dan uwansa Aminu Ado Bayero wanda aka ambaci sunan sa a matsayin Sarkin Kano[1][2][3] na shabiyar (15 ), bayan sauke dan uwansa kuma mai auren kanwarsa Muhammad Sanusi II da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje yayi . Kafin hawan sa kan kujerar sarauta, Bayero Chiroma ne na masarautar Kano kuma hakimin gundumar Nassarawa a lokacin mulkin Muhammad Sanusi II .
Nasiru Ado Bayero | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Masarautar Kano, 2 ga Faburairu, 1964 (60 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Ado Bayero | ||
Ahali | Aminu Ado Bayero | ||
Karatu | |||
Harsuna | Hausa | ||
Sana'a | |||
Sana'a | soja |
An haifi Nasiru Ado Bayero a ranar( 2 ) ga watan Fabrairu a shekara ta alif ɗari tara sittin da huɗu ( 1964 )a Kano, daga marigayi Ado Bayero wanda shi ne Sarkin Kano mafi dadewa a tarihin Kano . Shi ne da na uku ga marigayi Ado Bayero kuma shi ne dan fari, da aka haifa a gidan masarautar Kano da aka fi sani da gidan dabo. Ya m Siblings hada Sanusi Ado Bayero da tsohon Chiroma daga shekarar alif dari tara da casa'in (1990 )zuwa shekarar (2015) wanda ya daga baya ya yi nasara, da kuma Aminu Ado Bayero da 15th Sarkin Kano.[4]
Nasiru Ado Bayero ya yi karatun firamare da sakandire a Kano, daga nan ne ya wuce zuwa Jami'ar Maiduguri da ke Jihar Borno don karatun fannin sadarwa wato "Mass Communication" a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da bakwai (1987 ), ya kammala karatun Harvard Business School sannan kuma yana da satifiket a harshen Jamusanci a shekara ta alif dari tara da casa'in da uku ( 1993 ).[5][6]
Nasiru Ado Bayero ya samu gogewa wajen aiki tare da Bankin Kasuwancin Nahiyar Afirka, daga baya ya koma Kamfanin Coastal Corporation a Houston, Texas sai kuma Hamlet Investment Ltd London . Shine shugaban kamfanin Enclo Limited da kamfanin 9 Mobile Nigeria.
A ranar( 6 )ga watan mayu shekara ta (1994), an nada Nasir Ado Bayero a matsayin tafidan Kano kuma hakimin Waje daga mahaifinsa marigayi Ado bayaro Sarkin Kano na 13 sannan kuma daga baya ya sauya shi zuwa hakimin ƙaramar hukumar Nassarawa, sannan aka mayar da shi Tarauni a kan wannan matsayin. Ya samu daukaka zuwa Turakin Kano, da kuma Sarkin Dawakin Tsakargida a shekara ta (2000). A shekara ta (2015), Sarkin Kano na 14 Muhammad Sanusi II ya nada shi a matsayin Chiroman Kano.
A ranar (9 )ga watan Maris, a shekara ta (2019), Nasiru Ado Bayero ya hau kan karagar mulki bayan an naɗa ɗan uwansa Aminu Ado Bayero a matsayin Sarkin Kano na( 15 ).
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.