Mutuwa
From Wikipedia, the free encyclopedia
Mutuwa wani al'amari ne na dindindin, wanda ba'a iya maido shi baya a lokacin da rayuwa ta tsaya (ƙare), ga duk wata halitta wadanda ke rayuwa. Ana amfani da Kalmar mutuwa da kuma rashin iya yin aiki na kwakwalwa na dindin din a matsayin ma'anar mutuwa a hukunce. Gawar mamaci kan fara rubewa jim kadan bayan mutuwa.[1] Mutuwa abu ne da babu makawa, tsari ne na rayuwar duniya wanda daga qarshe yake faruwa ga dukkan wani abu mai rai.[2]
| |
Iri |
dakata de life (en) ƙunshiya property (en) de organism (en) |
---|---|
Sanadi | dying (en) |
Yana haddasa | dead (en) |
Hanyar isar da saƙo | |
Wasu abun | |
Lokacin mutuwa | |
Wurin mutuwa | |
Cause of death (en) | |
Manner of death (en) | |
Has part(s) (en) | |
cell death (en) single-organism process (en) multi-organism process (en) philosophy of death (en) |
Mutuwa ta kuma jibanci duk wani abu mai rai, gaba ɗaya tun daga ƙwayoyin halitta, da sassan jiki, raunin kwayoyin halitta. Wani abu ne da ba'a ɗauka a matsayin abu mai rai ba, kamar ƙwayar cuta, ana iya lalata ta amma ba a ce ta mutu ba.
Ya zuwa farkon karni na 21, sama da mutane 150,000 ke mutuwa a kowace rana a duniya.
Yawancin al'adu da addinai suna da fahimtan rayuwa bayan mutuwa, kuma suna riƙe da ra'ayin cewa akwai hukunci da lada don kyawawan ayyuka ko hukuncin zunubi don munana.