Shugaban kasa From Wikipedia, the free encyclopedia
Janar Murtala Muhammad (An haifeshi a cikin garin Kano, ranar 8 ga watan Nuwanban shekara ta alif ɗari tara da talatin da takwas 1938 AC) dake Kasar Hausa Arewacin Najeriya[1] (a jihar Kano),[2]yayi makarantar sa ne a makarantar da ake kira Royal Military Academy Sandhurst dake Kwalejin Barewa.[3]
Murtala Mohammed | |||
---|---|---|---|
30 ga Yuli, 1975 - 13 ga Faburairu, 1976 ← Yakubu Gowon - Olusegun Obasanjo → | |||
Rayuwa | |||
Cikakken suna | Murtala Ramat Muhammed | ||
Haihuwa | Kano, 8 Nuwamba, 1938 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Ƙabila | Mutanen Fulani | ||
Mutuwa | Lagos, 13 ga Faburairu, 1976 | ||
Yanayin mutuwa | magnicide (en) | ||
Killed by | Buka Suka Dimka | ||
Ƴan uwa | |||
Ahali | Balaraba Ramat Yakubu | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Royal Military Academy Sandhurst (en) Kwalejin Barewa | ||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | soja da ɗan siyasa | ||
Kyaututtuka | |||
Aikin soja | |||
Fannin soja | Sojojin Ƙasa na Najeriya | ||
Digiri | Janar | ||
Ya faɗaci |
Yaƙin basasar Najeriya Congo Crisis (en) | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Murtala Muhammad yana da yan uwa wanda ya haɗa da Balarabe Ramlat Yakubu. Janar Murtala Muhammad ya kasan ce yana jin yaruka biyu zuwa uku wanda suka hada da Hausa[4],Turanci[5] da kuma Yaren Pidgins na Najeriya.
Murtala Muhammad yana da Sana'a guda biyu Wanda ya hada da Soja kuma shi dan Siyasa[6] ne. A fannin Soja Murtala Muhammad ya kasan ce sojan ƙasa.
Murtala Muhammad yakai mukamin Janar a cikin gidan sojan ƙasa.
Murtala Muhammad ya kasan ce Bahaushe ne kuma Musulmi ne, baya ga haka kuma Murtala Muhammad ya kasan ce shugaba na kowa dake cikin ƙasar Najeriya wanda baya nuna bamban ci a tsakanin yare ko Addini ga duk mutanan ƙasar Najeriya hakan yasa ko Soja baya dashi me kula ko ace me take masa baya, hakan ne yabawa yan kudu dama suka hada kai da Buka Suka dinga binshi har masallaci bayan ya idar da sallah da kuma addu'o'in sa yana fitowa ya halbe shi da bindiga a hanyar shi ta komawa gida.
Murtala Muhammad ya mutu ne a cikin garin Legas dake tarayyar Najeriya a ranar (13) ga watan Faburairu a shekarar alif ɗari tara da saba'in da shida (1976). An kashe Murtala Muhammad ne bayan sallar asuba kuma an harbe shi ne da bindiga bayan ya fito masallaci a hanyar sa ta komawa gidan sa dake cikin garin Legas inda wani da ake kira Buka Suka Dimka ya halbe shi da bindiga. Wanda harbin bindigar yayi sanadiyyar ajalin sa har lahira Wanda da dama mutanen Najeriya sunyi jimamin rashin sa da akayi tare da yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi masa.
Allah ya jikan shi da Rahama ya kuma gafarta masa kura kuran sa baki ɗaya amin summa amin.
Murtala Muhammad ya mutu/rasu ne sanadiyar harbin sa da akayi da bindiga a shekara ta alif 1976.
Murtala ya kasan ce shugaban ƙasar Nijeriya ne daga watan Yuni shekara ta alif 1975 zuwa watan Fabrairun shekara ta alif 1976, bayan Yakubu Gawon-kafin Olusegun Obasanjo ya karɓi mulki).
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.