Masallacin Badshahi
From Wikipedia, the free encyclopedia
Masallacin Badshahi (harshen Punjabiبادشاہی مسجد), masallaci ne a birnin Lahore, babban birnin kasar Pakistan Wanda aka gina shi a zamanin daular Mughal.[1] Masallacin dai an gina shi ne a yammacin birnin Lahore saitin karkatar tsohuwar ganuwar birnin na Lahore,[2] kuma ana ganin masallacin a matsayin wata babbar alama ta birnin.[3]
Masallacin Badshahi | |
---|---|
Wuri | |
Ƴantacciyar ƙasa | Pakistan |
Province of Pakistan (en) | Punjab (en) |
Division of Pakistan (en) | Lahore Division (en) |
District of Pakistan (en) | Lahore District (en) |
Birni | Lahore |
Coordinates | 31°35′17″N 74°18′34″E |
History and use | |
Opening | 1671 |
Shugaba | Aurangzeb (en) |
Addini | Mabiya Sunnah |
Maximum capacity (en) | 100,000 |
Karatun Gine-gine | |
Material(s) | sandstone (en) |
Style (en) | Mughal architecture (en) |
Heritage | |
Parts | Hasumiya: 8 |
|
Gwarzo Jarumi Aurangzeb ne ya gina Masallacin a shekara ta 1671, wanda ya dauki shekaru biyu kafin kammala gina shi, sai a shekarar 1673 aka kamala. Masallacin wata babbar muhimmiyar alama ce dake nuna salo irin name gine-ginen zamanin Mughal. Shine ya rage daga cikin manyan masallatan da daular Mughal ta gina a kasar Pakistan.[4] Bayan rushewar daular Mughal, Masallacin ya koma karkashin ikon daular Sikh da kuma daular mulkin mallaka ta Birtaniya, Wanda a yanzu Masallacin ya zama wata babbar alama ta kasar Pakistan.