Gurin yin Ibadar mabiya Addinin Musulinci From Wikipedia, the free encyclopedia
Masallaci jam'i, ko Masallatai: wajene da musulmai ke bautan Allah (SWA) shikadai Ubangijin kowa da kowa.[1] Da Larabci[2] ana cewa Masjid. A wajen akasarin Musulmai[3], masallaci ya wuce wajen bautan Allah kadai. Musulmai na bauta tareda koyo da koyar da ilimin addinin Musulunci[4] tare da tattaunawa akan matsalolin musulmai tare da neman hanyar warware su a masallaci. A Birtaniya[5] masallatai ne cibiyar matattarar al'umar musulmai tare da koyar da addinin musulunci[4]. Anayin buku-kuwa da taruka a masallaci, musamman ma shagul-gulan daurin aure. Akwai dokokin yadda mutane zasu kasance a masallaci. Daya daga cikin su shine wani bazai takura ma wanda yake bauta ba. Masallatan farko an bude sune a karni na bakwai (7) a fili, amma daga baya an koma ana gina Masallatai a salon gini na Musulunci. Masallatan Quba da masallaci anabi farko farkon masallatai. Akwai masallatai a kowacce Nahiya in banda ta Antarctica.
masallaci | |
---|---|
building type (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | wajen bauta, religious building (en) da architectural structure (en) |
Facet of (en) | Islamic architecture (en) |
Addini | Musulunci |
Abubuwan da aka hana a wajen | please take off your shoes (en) |
Ana gina Masallatai ne a yanayin gine-gine irin na Musulunci a bisa akasari, amma kuma yawancin salon ginin masallatai ya danganta ne ga irin yadda salon ginin kasashe da al'adun mutane.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.