Maganin gargajiya
From Wikipedia, the free encyclopedia
Magungunan Gargajiya (wanda kuma akafi sani da likitan ƴan ƙasa ko likitancin jama'a ). Ya kasance wan nan ya ƙunshi fannonin likitanci na ilimin gargajiya, waɗanda suka bunƙasa tsawon tsararraki a cikin aƙidar al'ummomi daban-daban, gami da ƴan asalin ƙasar, kafin lokacin maganin zamani. Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ayyana. Maganin gargajiya a matsayin “jimlar ilimi, fasaha, da ayyuka bisa ka’idoji, imani, da gogewa na asali ga al’adu daban-daban, ko an bayyana ko a’a, da ake amfani da su wajen kula da lafiya haka nan. kamar yadda yake a cikin rigakafi, tantancewa, ingantawa ko magance cututtukan jiki da na tabin hankali”. [1] Magungunan gargajiya sau da yawa ana bambanta da likitan ilimin kimiyya.
Maganin gargajiya | |
---|---|
system of medicine (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | medicine (en) da alternative medicine (en) |
Bangare na | traditional, complementary and integrative medicine (en) |
A wasu kasashen Asiya da Afirka, kusan kashi 80 cikin 100 na al'ummar kasar sun dogara ne da magungunan gargajiya domin bukatunsu na farko na kiwon lafiya . Lokacin da aka ɗauke shi a waje da al'adun gargajiya, ana ɗaukar magungunan gargajiya a matsayin wani nau'i na madadin magani . [1] Ayyukan da aka fi sani da magungunan gargajiya sun haɗa da magungunan gargajiya na Turai, magungunan gargajiya na kasar Sin, magungunan gargajiya na Koriya, magungunan gargajiya na Afirka, Ayurveda, magungunan Siddha, Unani, magungunan gargajiya na Iran, magungunan Musulunci na tsakiya, Muti, da Ifá . Sana'o'in kimiyya da ke nazarin likitancin gargajiya sun hada da herbalism, ethnomedicine, ethnobotany, da kuma ilimin halin ɗan adam .
WHO ta lura cewa, duk da haka, "yin amfani da magungunan gargajiya ko ayyuka marasa dacewa na iya haifar da mummunan tasiri ko haɗari" kuma " ana buƙatar ƙarin bincike domin tabbatar da inganci da aminci" irin waɗannan ayyuka da tsire-tsiren masu magani da tsarin magungunan gargajiya ke amfani da su. [1]A sakamakon haka, WHO ta aiwatar da dabarun shekaru tara domin taimakawa kasashen mambobin kungiyar domin samar da manufofi masu tasiri da aiwatar da tsare-tsaren ayyuka da za su karfafa rawar da magungunan gargajiya ke takawa wajen kiyaye lafiyar jama'a.[2]