![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/9/90/Braider_at_a_hair_salon.jpg/640px-Braider_at_a_hair_salon.jpg&w=640&q=50)
Kitso
From Wikipedia, the free encyclopedia
Kitso wata al'ada ce da ake yinta domin tufke gashin kai, saboda ado ko kwalliya ko kuma dalili na Addini. A wasu kasashen akasari mata suka fi yin kitso, yayinda a wasu kasashen maza kadai suka fi yin sa. A wasu kuma maza da mata ne ke yin kitso sai a al'ada kasar Hausa Mata su ne keyin kitso ba maza ba, idan ka ga namiji da kitso to lallai ya saba wa al'adun Hausawa da kuma Addinin Musulunci. Mata na kitse gashin kan su don Kwalliya da birge mazajensu na aure da ma samarinsu kafin aure, kitso yana da matukar muhimmanci sosai musamman ga wasu kabilun Afrika. Amma a al'adance ko kuma a al'adar Hausawa kitso mata ke yi ba maza ba, idan har ka ga namiji da kitso to lallai dan daudu ne kuma ya saba wa Addinin Musulunci, su ma matan akwai inda yake saba wa Addinin Musulunci a yayinda suka nemi kara gashin kansu, wannan haramun ne a Musulunci ko ma da a ce babu haramci to masana sun tabbatar da karin gashi na kawo zubewarsa da mayar da kan mata mai sanƙo.[1][2][3][4]
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/9/90/Braider_at_a_hair_salon.jpg/640px-Braider_at_a_hair_salon.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/84/Peul_women_in_Paoua.jpg/640px-Peul_women_in_Paoua.jpg)
![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
siffa da style (en) ![]() |
Filin aiki |
fashion (en) ![]() |
Has contributing factor (en) ![]() |
haircutting (en) ![]() |
Wasu matan ma sukan dauki kitso a matsayin sana'ar su ta yau da kullum kuma suna samun amfani. Kitso kala-kala ne, akwai na gargajiya da na zamani.[5]