From Wikipedia, the free encyclopedia
Julia Sebutinde alkaliys ƴar ƙasar Uganda da ke zamanta na biyu a kotun duniya bayan sake zaɓenta da akayi a ranar 12 ga Nuwamba, shekarar 2020. Ita ce kuma shugabar Jami'ar Muteesa I Royal (Muteesa I Royal University) a halin yanzu jami'ar mallakar masarautar Buganda. Ta kasance alkaliya a kotun tun a watan Maris shekarar 2012. Ita ce mace ta farko a Afirka da ta zauna a kotun ICJ.[1][2] Kafin a zaɓe ta a ICJ, Sebutinde ta kasance alkaliya ta Kotun Musamman a Saliyo. An naɗa ta a wannan muƙamin a shekarar 2007.Es dura.
Julia Sebutinde | |||
---|---|---|---|
6 ga Faburairu, 2012 - ← Abdul Koroma (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Entebbe (en) , 28 ga Faburairu, 1954 (70 shekaru) | ||
ƙasa | Uganda | ||
Ƙabila | Yahudawa | ||
Karatu | |||
Makaranta |
University of Edinburgh (en) Makarantar Sakandare ta Gayaza Jami'ar Makerere University of Edinburgh School of Law (en) | ||
Harsuna |
Turanci Ibrananci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | mai shari'a da Lauya |
An haife ta a yankin Tsakiyar Uganda mahaifiyar ta ma'aikaciyar gwamnati kuma uwargida mai suna Semambo.Ta halarci Makarantar Firamare ta Lake Victoria a Entebbe a cikin ƙarnin 1960s.[3] Daga nan ta shiga makarantar sakandare ta Gayaza sannan ta koma King’s College Budo, kafin ta shiga jami’ar Makerere ta karanta fannin shari’a. Sebutinde ta kammala karatun digiri a fannin Shari'a (Bachelor of Laws) a shekarar 1977. Ta samu Diploma a fannin Shari'a daga Cibiyar Bunkasa Shari'a da ke Kampala a shekarar 1978. A cikin shekarar 1990, ta yi rajista a Jami'ar Edinburgh don karatun digirin-digirgir a fannin Shari'a (Master of Laws), ta kammala karatunta a shekarar 1991. A cikin 2009, don karrama aikinta da kuma gudummawar da take bayarwa ga adalci na ƙasa da ƙasa, Jami'ar Edinburgh ta ba ta lambar girmamawa ta zama dakta duk dai a fannin Shari'a (Doctor of Law).[4][5]
Julia Sebutinde ta fara aiki a ma'aikatar shari'a a gwamnatin Uganda daga 1978 zuwa 1990. Bayan ta kammala karatunta a Jami'ar Edinburgh a shekarar 1991, ta yi aiki a ma'aikatar Commonwealth a Burtaniya. Daga baya ta shiga ma’aikatar shari’a a jamhuriyar Namibiya, wadda ta samu ƴancin kai a wancan lokacin. A cikin shekarar 1996, an naɗa ta alkaliya a babbar kotun Uganda.A wannan matsayi, ta jagoranci kwamitocin bincike guda uku da suka shafi ma'aikatun gwamnati kamar haka:
A cikin 2005 an nada mai shari'a Julia Sebutinde, tare da zama na biyu daga gwamnatin Uganda, zuwa Kotun Musamman a Saliyo, wanda Majalisar Dinkin Duniya ta kafa.Daga baya aka nada ta a matsayin shugabar alkali a kotun sauraron kararrakin zabe II, a wancan lokacin da ke da alhakin sauraron karar da ake yi wa tsohon dan kasar Laberiya, Charles Taylor.A wannan matsayi ta ki halartar zaman ladabtarwa a kan lauyan Taylor, lamarin da ya kai ga rashin da'a na shari'a, amma har yanzu kotun ta musamman ta Saliyo ba ta amince da hakan ba.[6][7]
A cikin zaɓen alkalan ICJ, na shekarar 2011.[8] Sebutinde ta kasance ɗaya daga cikin ƴan takara takwas na kujerun shari'a guda biyar a Kotun Duniya. waɗanda ƙungiyoyin ƙasa na Croatia, Denmark, da Uganda suka gabatar da su a cikin Kotun Din-din-din na Arbitration.[9] A zaɓen, ɗan takara mai nasara yana bukatar cikakken rinjayen ƙuri'un a zauren Majalisar Dinkin Duniya da kuma na Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya. A ranar farko da aka kaɗa ƙuri’a an zaɓi ƴan takara huɗu amma ba a cika na biyar ba.[10][11] A lokacin da aka ɗage kaɗa ƙuri'ar, Abdul Koroma, dan takara daga Saliyo, ya samu ƙuri'u 9 daga cikin 15 na Kwamitin Sulhu, da ƙuri'u 8 da ake buƙata don zaɓen. A Majalisar Dinkin Duniya, bayan zagaye biyar na jefa ƙuri'a, Julia Sebutinde, ƴar takarar, ta samu ƙuri'u 97 daga cikin 193, da ƙuri'u 97 da ake buƙata don zaɓe.[12][13] A lokacin da aka ci gaba da kaɗa ƙuri'a a ranar 13 ga watan Disamba, shekarar 2011, Sebutinde ta samu cikakken rinjayen ƙuri'u a kwamitin sulhu da na Majalisar Dinkin Duniya, don haka aka ayyana ta a matsayin zaɓaɓɓiya kuma wadda tayi Nasara a zaɓen.[14]
Julia Sebutinde ta auri John Bagunywa kuma har yanzu suna tare sun samu ƴaƴa mata biyu. Ana cewa tana matuƙar son kiɗa, ƙwallon ƙafa da kuma iyo. Tana jin daɗin abincin Indiya da abinci mai yaji. Justice Sebutinde ita ce shugabar Jami'ar Kimiyyar Kiwon Lafiya ta Duniya, a Kampala, matsayin da ta riƙe tun 2008.[15]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.