Harin bama-bamai a Najeriya From Wikipedia, the free encyclopedia
A ranar 20 ga watan Mayun shekara ta 2014, wasu bama-bamai biyu sun tashi a birnin Jos na jihar Filato a Najeriya, inda suka kashe mutane aƙalla 118 tare da jikkata wasu fiye da 56.[1] Bam na farko ya tashi ne a wata kasuwa, na biyu kuma kusa da wata tashar mota. Ko da yake babu wata ƙungiya ko wani mutum da ya ɗauki alhakin kai hare-haren, ana danganta hare-haren da ƙungiyar Boko Haram,[2] wacce tayi ƙaurin suna na kai hara hare da dama a Najeriya, musamman yankin arewa maso gabashin ƙasar.
| ||||
Iri |
aukuwa car bombing (en) | |||
---|---|---|---|---|
Kwanan watan | 20 Mayu 2014 | |||
Wuri | Jos | |||
Ƙasa | Najeriya | |||
Adadin waɗanda suka rasu | 118 | |||
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 56 |
Kiristoci da Musulmai sun yi arangama da dama a birnin Jos acikin shekaru da dama kafin tashin bama-bamai, kuma ƙungiyar ta Boko Haram ma ta yi ta kai ruwa rana kafin harin.[1] A shekarar 2012, ƙungiyar Boko Haram ta kai wa wasu majami'u hari da bama-bamai da nufin assasa rikicin addini tsakanin Kirista da Musulmi.[1] A cikin watan da ya gabato harin Boko Haram, na sace 'yan matan makaranta sama da 200, [1] ko da yake birnin Jos ya fuskanci manyan hare-hare guda biyu tun daga shekara ta 2012.[1] Kwana ɗaya bayan tashin bama-baman an kashe mutane 27 a hare-haren wasu kauyuka.[2]
Fashewar bama-baman kwara biyu sun kasance mintuna 30 tsakani,[1] ɗaya ya fashe da karfe 3:00, ɗayan kuma da ƙarfe 3:30.[3] Fashewar farko ta faru ne a Kasuwar Terminus, inda aka samu asarar rayuka sama da hamsin.[4] A cikin Terminus akwai "asibitin koyarwa, shaguna, ofisoshi da kasuwa" kafin harin. [5] Na biyu ya faru ne a kusa da wani asibiti. [4] Kuma ya kashe masu aikin ceto, waɗanda suka je taimakawa bayan tashin bam na farko. [1] An kuma ga yadda hayaki mai yawa ya turnike wurin. [4] Mai yiyuwa ne an shirya tashin bama-baman ne domin yin sanadin asarar rayuka da dama.[1] Bam ɗin da aka ɗana a cikin motar ya sa motocin da ke kusa da wurin suka tarwatse.[5]
Jami’an kashe gobara da masu aikin ceto sun yi ƙoƙarin isa wuraren da bama-baman suka tashi, amma “dubban” mutane ne ke tserewa daga yankin.[1] An sanya bama-baman don kashe mutane da yawa, ba tare da nuna bambanci ba na addini [1] ta hanyar amfani da dabara, (ta kashe mutane, bayan anzo ana ceton waɗanda suka jikkata, sai kuma a tashi bam na biyu da zai yi sanadiyar mutuwar Mutanen wurin ciki hard waɗanda suka je bada agajin gaggawa).[3][1] Sojoji sun kafa shingayen binciken ababen hawa a yankin, inda wasu suka gudanar da binciken ababen hawa. Ana sa ran adadin gawarwaki zai ƙari, [5] kuma an ƙona wasu gawarwakin da ba a iya tantance su ba.[3] Adaɗin waɗanda suka mutu ya kai 46 cikin sauri zuwa adadi na 118 yayin da aka share baraguzan ginin wuraren da suka ruguje.[3] Duk da haka, wasu sun ƙiyasta adadin ya kai 150.[6]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.