From Wikipedia, the free encyclopedia
Maria de Fátima da Veiga (an haife ta a ranar 22 ga watan Yuni, 1957) 'yar siyasa ce kuma jami'ar diflomasiya ta Cape Verde. Veiga ta kasance ministan harkokin waje daga shekarun 2002 zuwa 2004. Ita ce mace ta farko ministar harkokin wajen ƙasar a tarihin Cape Verde.
Fátima Veiga | |||
---|---|---|---|
2002 - 2004 | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | São Vicente (en) , 22 ga Yuni, 1957 (67 shekaru) | ||
ƙasa | Cabo Verde | ||
Karatu | |||
Makaranta | University of Provence - Aix-Marseille I (en) | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya | ||
Kyaututtuka |
An haifi Veiga a tsibirin São Vicente. Daga baya ta halarci wasu manyan makarantun da suka haɗa da Jami'ar Aix-en-Provence da ke kudancin Faransa, gidauniyar Jamus a Berlin, Prague da kuma a Brazil. A cikin shekarar 1980, ta fara aiki a ma'aikatar harkokin waje ta Cape Verde. Tsakanin shekarun 2001 da 2002, ta kasance Jakadiyar Cape Verde a Cuba. Lokacin da ta kasance ministar harkokin waje, ta ziyarci Paris daga ranar 9 zuwa 12 ga watan Janairu, 2002.
Shekaru kaɗan a cikin shekarar 2007 ta kasance Jakadiyar Cape Verde a Amurka. Ta gabatar da takardun shaidarta ga Shugaba George Bush a ranar 16 ga watan Agusta, 2007. [1]
Tun a watan Fabrairu 20, 2014, ita ce jakadiyar Capeverdean a Faransa. Ta gaji José Armando Filomeno Ferreira Duarte wanda shi ne jakada mafi daɗewa a Faransa.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.