Filin shakatawa na W (Faransanci: Parc national du W)[1] ko Yankin shakatawa na W (Faransanci: W du Niger) babban filin shakatawa ne a Afirka ta Yamma a kusa da bakin ruwa a Kogin Niger mai kama da harafin W (Faransanci: double v). Dajin ya haɗa da yankuna na kasashen uku Niger, Benin da Burkina Faso, kuma gwamnatocin ukun ne ke kula da shi. Har zuwa shekara ta 2008, aiwatar da tsarin gudanarwar yanki ya sami tallafi daga aikin ECOPAS na Kungiyar EU (Kare Tsarin Yanayi a Sudano-Sahelian Afirka, Faransanci: Ecosystèmes protégés en Afrique soudano-sahélienne). Gidajen shakatawa guda uku suna aiki a ƙarƙashin sunan W Transborder Park. (Faransanci: Parc Yankin W).[2] Bangaren Filin shakatawa na W da ke kwance a Benin, wanda yakai sama da 8,000 km2 (3,100 sq mi), ya zo karkashin cikakken kulawar Parks na Afirka a watan Yunin 2020.[3] A cikin Benin, W National Park yana haɗuwa da Pendjari National Park wanda shima yana ƙarƙashin kulawar Parks na Afirka.
Quick Facts Bayanai, Bangare na ...
Kulle