Filin jirgin saman Dubai
From Wikipedia, the free encyclopedia
Filin jirgin saman Dubai (IATA: DXB, ICAO: OMDB) shi ne babban filin jirgin saman da ke birnin Dubai, a masarautar Dubai, a ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE). kuma shine filin jirgin saman da yafi kowane filin jirgi sufurin mutane na tsakanin kasa da kasa a duniya.[1] kuma shine na hudu a hada-hadan jama'a a duniya.[2] kuma na bakwai a sufurin hajoji a duniya, sannan shine filin jirgin da yafi kowane a zurga-zurgan Airbus A380 da Boeing 777,[3] kuma jiragensa yafi kowane akasarin sufurin fasinjoji a duk tashi.[4] a shekara ta 2017, DXB sun daukin nauyin pasinjoji miliyan 88, da hajoji masu kimanin nauyin tonnes miliyan 2.6 kuma sunyi rijistan zurga-zurgan jirage na kimanin dubu 409,493.[5]
Filin jirgin saman Dubai | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
مطار دبي الدولي | |||||||||||||||||||||||
Wuri | |||||||||||||||||||||||
Ƴantacciyar ƙasa | Taraiyar larabawa | ||||||||||||||||||||||
Haɗaɗɗiyar daular larabawa | Dubai | ||||||||||||||||||||||
Mazaunin mutane | Al Garhoud (en) | ||||||||||||||||||||||
Coordinates | 25°15′10″N 55°21′52″E | ||||||||||||||||||||||
Altitude (en) | 62 ft, above sea level | ||||||||||||||||||||||
History and use | |||||||||||||||||||||||
Ƙaddamarwa | 1960 | ||||||||||||||||||||||
Mai-iko | Dubai | ||||||||||||||||||||||
Manager (en) | Dubai Airports Company | ||||||||||||||||||||||
Suna saboda | Dubai (birni) | ||||||||||||||||||||||
Karatun Gine-gine | |||||||||||||||||||||||
Yawan fili | 1,400 ha | ||||||||||||||||||||||
Filin jirgin sama | |||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||
City served | Dubai (birni) | ||||||||||||||||||||||
Flights |
| ||||||||||||||||||||||
Parts | airport terminal (en) : 3 | ||||||||||||||||||||||
Offical website | |||||||||||||||||||||||
|
Babban filin jirgin sama na Dubai yana nan a gabacin Al Garhoud district, 2.5 nautical miles (4.6 km; 2.9 mi) dake Dubai kuma ya mamaye fili mai girman eka 7,200 (hekta 2,900).[6] Ginin Terminal 3 shine gini na biyu a girma a duniya a fadin kasa. kuma shine mafi girman terminal na filayen jirage a duniya.[7]A watan Julin shekara ta 2019, Filin Jirgin ta sanya mafi girman naurar wuta mai amfanmi da hasken rana a yankin filin jirgin a matsayin daya daga cikin burikan gwamnatin Dubai na rage shan wutan nepa a kasan zuwa sheakara ta 2030.[8]
Filin jirgin Emirates na da nata cibiyar a tashar filin jirgin sama a Filin jirgin sama na dubai (DXB) da kuma wani a Terminal 3 tare da wasu bangarori 3 da suke hadin gwiwa da Flydubai. Tashar Filin jirgin Emirates shi ne mafi girman tasha a Gabas-ta-tsakiya.