sana'ar kamun dabbobi From Wikipedia, the free encyclopedia
Farauta Sana'a ce dadadda, wanda aka gada tun iyaye kaka, da kakanni, musamman a kasar Hausa. Kuma kusan ace farauta ita ce sana'a ta farko a kasar Hausa kafin zuwan wasu sana'o'in kamar su kiwo, noma, Su, da dai sauran sana'o'i. Kuma wasu suna ganin cewa ita farauta kai tsaye tana nufin (Nema) haka zakaji wasu suna cewa idan kuma zasu fita gida don zuwa kasuwa ko wani wurin neman abinci, sai kaji sunce "mun fita (farauta) wato nema" haka kuma mata a cikin gida idan mazajen su zasu fita sai kaji suna cewa a farauto da yawa. A takaice dai farauta na nufin. Nema. Amma a zahiri farauta na nufin fita daga gida zuwa daji don neman namun daji da kuma tsuntsaye da sauransu, Mafi yawanci maza ne aka fi sani da sana'ar farauta. suna shiga daji don farauto dabbobin daji,daban daban ko da yake kuma ana samun kadan daga cikin mata masu kamar maza suna fita farauta. Akan fita farauta wuni daya, kwana daya har zuwa watanni.[1][2]ana Amfani da karnuka da bindigu, kwari da baka, abin kai bugu domin gudanar da farautar.
| |
Iri | aiki |
---|---|
Bangare na | primitive tribal community (en) |
Kwanan watan | 1,800,000 years BCE – |
Participant (en) | |
Has part(s) (en) | |
seeking (en) collecting (en) attack (en) butchering (en) |
Da dai sauransu akan farauto irin su Zomo, barewa, gada da sauran su. Mafi yawancin mafarauta sunada magunguna sosai (tambaya) saboda kwankwaman namun jeji. Mafarauci shine tilon mai sana'ar farauta mafarauta kuma jam'in masu yin farauta.[3]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.