![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/c/cd/Arne_Slot.jpg/640px-Arne_Slot.jpg&w=640&q=50)
Arne slot
From Wikipedia, the free encyclopedia
Arend Martijn "Arne" Slot (An haifeshi a ranar 17 September 1978).[1] Kwararren mai bada horo ne na kasar Dutch. Sannan kuma tsohon dan wasa wanda yanzu haka yake horas da kungiyar kwallon kafa ta Liverpool.
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/c/cd/Arne_Slot.jpg/640px-Arne_Slot.jpg)
Slot ya buga kwallo a matsayin dan wasan tsakiya a kungiyar F. C Zwolle inda yaci gasar Eeste Divisie a shekarar alif 2002 da NAC Breda da kuma Spata Rottedam. Kafin ya ajiye kwallon kafa ya dawo kungiyar PEC Zwolle inda ya kara cin wani kofin na gasar Eeste Divisie a shekarar alif 2012.
Ya fara yin rayuwa a matsayin mai bada horo a cikin akadami ta kungiyar kwallon kafa ta PEC Zwolle a matsayin mataimaki, daga baya kuma ya zama kocin kungiyar akademi din a shekarar alif 2017. Daga baya kuma ya zama mataimakin mai bada horo a kungiyar kwallon kafa ta AZ kuma ya zama kocin kungiyar a shekara ta alif 2019. Slot ya zama kocin kungiyar kwallon kafa ta Feyenoord a shekarar alif 2021. Ya jagoranci kungiyar har zuwa wasan karshe na gasar UEFA Europa Conference. Ya cima kungiyar gasar Eridivisie da kofin KNVB duk a shekarar.