From Wikipedia, the free encyclopedia
Amina Jane Mohammed[1] (an haife ta a ranar 27, ga watan Yunin shekara ta alif ɗari tara da sittin da ɗaya, 1961), ta kasance ƴar siyasan Najeriya da Birtaniya ce, wadda itace Mataimakiyar Babban Sakatare na Majalisar Ɗinkin Duniya. Gabanin ta riƙe Ministar Muhalli a tarayyar Najeriya tsakanin shekara ta dubu biyu da goma sha biyar, 2015, da shekarar dubu biyu da goma sha shida, 2016.[2]
Amina J. Mohammed | |||||
---|---|---|---|---|---|
28 ga Faburairu, 2017 - ← Jan Eliasson (en)
11 Nuwamba, 2015 - 15 Disamba 2016 ← John Odey - Ibrahim Usman Jibril → | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | Liverpool, 27 ga Yuni, 1961 (63 shekaru) | ||||
ƙasa | Najeriya | ||||
Karatu | |||||
Makaranta | University of Reading (en) | ||||
Harsuna |
Turanci Pidgin na Najeriya | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||
Mahalarcin
| |||||
Employers |
Majalisar Ɗinkin Duniya Columbia University (en) | ||||
Kyaututtuka |
gani
| ||||
Mamba | American Academy of Arts and Sciences (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Musulunci |
An haifi Amina Jane Mohammed a Liverpool, dake England, a United Kingdom a ranar 27, ga watan Yunin shekara ta alif ɗari tara da sittin da ɗaya, 1961[3] ga iyaye likitan dabbobi da kuma mahaifiya mai kula da majinyata (nurse) 'yan asalin harshen Hausa-Fulani daga Najeriya.[4]
Amina ta halarci makarantar firamare na Kaduna da birnin Maiduguri a Najeriya, sai kuma makarantar Makarantar "The Buchan School" da ke tsibirin Isle of Man.[5]Daga bisani ta halarci kwalejin Henley Management College a 1989.[6]Bayan ta kammala karatun ta ne mahaifinta ya nemi ta da ta dawo gida Najeriya.[7]
A tsakanin shekarun, 1981, zuwa 1991, Amina tayi aiki da "Archcon Nigeria", wani kamfanin zane-zane da suke da alaka da kamfanin zane-zane na Norman and Dawbarn da ke United Kingdom.[8] A shekara ta, 1991, ta samar da kamfanin Afri-Projects Consortium, sannan daga shekara ta, 1991, zuwa 2001, itace darekta mai zartarwa na kamfanin.[9]
Daga shekara ta, 2002, har zuwa shekara ta, 2005, Amina ta shirya wani gangami da ilimantarwa game da jinsi karkashin United Nations Millennium Project.[10]
Amina ta rike matsayin mataimakiya na musamman ( Senior Special Assistant) na shugaban kasa akan shirin Millennium Development Goals (MDGs). A cikin shekara ta, 2005, an zarge ta da amfani da kudin tallafi na kasa a wajen ayyukan MDGs.
Amina ta kasance wacce ta kafa kuma ta samar da kamfanin Center for Development Policy Solution, sannan kuma a matsayin farfesa na daliban masters a jami'ar Columbia. A tsakanin wannan lokaci, tayi aiki a matsayin mai bada shawarwari na kungiyoyi daban daban na duniya wanda ya hada da, babban sakatariya a Majalisar Dinkin Duniya (UN) don zama na musamman akan Post-a shekara ta, 2015 "Development Agenda"; da kuma Independent Expert Advisory Group.
Sannan har wayau ta rike matsayin chairman na majalisin United Nations Educational, Scientific and Cultural Organization (UNESCO), sashin bincike da bayanai akan ilimi na duniya "Global Monitoring Report on Education" (GME).[11]
Har zuwa shekara ta, 2012, Amina tana daya daga cikin muhimman mutane a taron e Post-a shekara ta, 2015, Development Agenda, inda take aiki a matsayin mai bada shawara na musamman ga shugaban majalisar dinkin duniya watau Ban Ki-moon,[12][13] sannan tana daga cikin mutane na musamman na "High Level Panel of Eminent Persons (HLP)" da majalisar Open Working Group (OWG) da dai sauransu.[14] Daga shekara ta, 2014, tayi aiki a matsayin babban sakatariya na "ndependent Expert Advisory Group on the Data Revolution for Sustainable Development".[15]
Amina tayi aiki a matsayin ministan muhalli a karkashin mulkin shugaba MUhammadu Buhari daga watan Nuwamaban shekara ta, 2015, zuwa watan Febrerun shekara ta, 2017.[16] A wannan lokaci itace wakiliyar Najeriya a Kungiyar Kasashen Nahiyar Afurka wato "African Union (AU)" fannin jawo canji wanda Paul Kagame ke jagoranta.[17] Ta ajiye aiki da kungiyar Nigerian Federal Executive Council a ranar 24, ga watan Febrerun shekara ta, 2017.[18]
A cikin shekara ta, 2017, wata kungiya mai zaman kanta ta zargi Amina da cewa tana ba da izini ga kamfanonin kasar China wajen diban itace timber zuwa kasashensu ba tare da izinin gwamnatin tarayya ba, a lokacin tana ministan muhalli na Najeriya.[19][20][21]Amma daga bisani gwamnatin Najeriya ta karyata zargin.[22]
Aure
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.