Polio
From Wikipedia, the free encyclopedia
(Poliomyelitis), a harshen Turanci wato Cutar Polio ko kuma Cutar shan inna, cuta ne da ake iya dauka daga wani ta dalilin kwayoyin cutar polio (poliovirus).[1] Kusan kaso 75% na cutar basa nuna alamomin cutar;[2] ana iya samun kananan alamomi kamar ciwon makoshi da zazzabi; a yawancin lokuta alamomi kan tsananta kamar ciwon kai, ciwon wuya, da kuma Paresthesia.[1][3] Wadannan alamomi sukan wuce a tsakanin mako daya ko biyu.[1] Alamar gama-gari itace shanyewar sashin jiki na dundundun, da kuma mutuwa a wasu lokuta idan tayi tsanani.[1] Ana iya samun alamomin cutar (post-polio syndrome) shekaru kadan bayan warke daga cutar, da kuma habakar karancin karfi gabbai irin wanda mutum ke fuskanta yayin kamuwa cutan.[4]
Polio | |
---|---|
Description (en) | |
Iri |
viral infectious disease (en) , peripheral neuropathy (en) , acquired motor neuron disease (en) , central nervous system viral disease (en) , Enterovirus infectious disease (en) cuta |
Specialty (en) |
infectious diseases (en) , neurology (en) orthopedics (en) |
Sanadi | poliovirus (en) |
Symptoms and signs (en) |
muscle weakness (en) , paralysis (en) , paresis (en) , meningism signs (en) , zazzaɓi, amai gudawa |
Effect (en) |
Otter Valley polio epidemic (en) 1916 polio epidemic (en) |
Disease transmission process (en) |
fecal–oral route (en) contact transmission (en) |
Physical examination (en) |
physical examination (en) , viral culture (en) Q25438941 |
Suna saboda | Jakob Heine (en) da Karl Oskar Medin (en) |
Identifier (en) | |
ICD-10-CM | A80.9, A80, A80.3, A80.2, A80.4, A80.1 da A80.0 |
ICD-9-CM | 045, 045.9, 045.92 da 045.90 |
DiseasesDB | 10209 |
MedlinePlus | 001402 |
eMedicine | 001402 |
MeSH | D011051 |
Disease Ontology ID | DOID:4953 |
Cutar shan inna na faruwa ne hakanan ne ga dan-Adam.[1] Tana da saurin yaduwa matuka, kuma tana yaduwa daga wani zuwa wani ta hanyar cudanya ta baki ko fuska[1][5] (misali a dalilin gurbataccen muhalli, ko kuma ta hanyar cin abinci ko shan ruwa da ke dauke da kashin dan-adam), ko kuma ta hanyar cudanya ta baki da baki.[1] Wadanda suka kamu da cutar suna iya yadata ga sauran mutane har tsawon makonni shida ko da ace basu fara nuna wasu alamomi ba.[1] Ana iya gano asalin cutar ta hanyar nemo kwayar cutar a cikin kashin mutum ko kuma nemo kwayoyin halitta masu fada da kwayoyin cuta acikin jini.[1]
Poliomyelitis (kwayoyin cutar shan inna) sun wanzu na tsawon shekaru dubunnai da suka gabata, tare da nuna cutar acikin zanukan zamunan baya.[1] Wanda ya fara gano wannan cutar wani masanin magunguna ne bature dan Ingila Michael Underwood a matsayin cuta mai rudarwa acikin shakarar 1789,[1][6] sannan kuma an fara gano kwayoyin cutar da ke janyo cutar a shekarar 1909, wanda wani mai binciken kwayoyin kariyar jiki dan kasar Austriya Karl Landsteiner.[7][8] An samu manyan barkewar cutar acikin karni na 19 a kasashen Turai da Amurka,[1] sannan acikin karni na 20, cutar ta zamonta cuta mafi tada hankali acikin cututtukan da ke kama kananan yara.[9] Bayan gano rigakafin cutar acikin shekarun 1950s, cutar shan inna ta ragu acikin sauri.[1]