Waina abinci ne mai sauƙi wanda kuma aka sani da Masa. Tasa ce da za a iya shirya ta da farin Masara ko Rice na gida. An fi shirya ta a Arewacin Najeriya kuma ana cin ta tare da Miyan Waina/Taushe.
Masa abinci ce wacce aka fi sani da suna Waina, kuma yana ɗaya daga cikin abincin gargajiya, Musamman a Kasar Hausa. Abinci ne wanda aka fi cin shi da safe kuma ana cin shi a koda yaushe.