Remove ads
From Wikipedia, the free encyclopedia
Hukumar Yiwa Kasa Hidima (NYSC) wani shiri ne da gwamnatin Najeriya ta kafa a lokacin mulkin soja domin shigar da daliban Najeriya da suka kammala karatu a fannin gina ƙasa da kuma ci gaban ƙasar. Babu aikin soja a Najeriya, amma tun daga shekarar 1973, an buƙaci waɗanda suka kammala karatu a jami'o'i da kwalejin kimiyya da fasaha su shiga shirin bautar ƙasa na tsawon shekara ɗaya.[1] Ana san hakan a matsayin shekarar hidimtawa ƙasa. Ahmadu Ali ya taɓa zama Darakta-Janar na hukumar yiwa kasa hidima wato (NYSC) na farko har zuwa shekara ta 1975.[2] Darakta-Janar mai ci a yanzu shi ne Yusha'u Dogara Ahmed.[3]
Hukumar Yiwa Kasa Hidima | |
---|---|
| |
To foster national unity & cohesion | |
Bayanai | |
Suna a hukumance |
National Youth Service Corps |
Gajeren suna | NYSC |
Iri | ma'aikata da government organization (en) |
Ƙasa | Najeriya |
Mulki | |
Hedkwata | Abuja |
Tsari a hukumance | government agency (en) |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 22 Mayu 1973 |
Wanda ya samar | |
nysc.gov.ng |
An naɗa Manjo Janar Suleiman Kazaure a matsayin darakta janar na hukumar yiwa kasa hidima, NYSC a ranar 18 ga Afrilu 2016 kuma ya kasance shugaban na 17 na shirin har zuwa ranar 26 ga watan Afrilun 2019 da aka mayar da shi cibiyar samar da albarkatun ƙasa ta Najeriya.
An kirkiro NYSC ne a ranar 22 ga watan Mayu, 1973 a lokacin mulkin Janar Yakubu Gowon a matsayin hanyar sulhu, sake gina, da sake gina kasa bayan Yaƙin basasar Najeriya. An kafa ta ne bisa doka mai lamba 24, wadda ta bayyana cewa, an ƙirƙiro wannan shiri ne "da nufin karfafawa da bunƙasa alaƙa tsakanin matasan Najeriya da kuma inganta haɗin kan ƙasa".[4]
Ana tura membobin ƙungiyar (masu shiga shirin bautar ƙasa) zuwa jihohin da ba jiharsu ta asali ba, inda ake sa ran za su yi cuɗanya da jama’a kama daga ƙabilu daban-daban, zamantakewa da iyali, su koyi al’adun ’yan asalin wurin da aka kai su. Wannan mataki na kuma nufin samar da haɗin kai a ƙasar da kuma jin daɗin sauran ƙabilu.
Matasan Najeriya da suka cancanci yin hidimar ana sa ran za su yi rajista a shafin intanet na hukumar NYSC, domin a kira su yin hidima. Bayan rajista, matasan da suka cancanta suna samun wasiƙar kira, wanda ke nuna halin da suke ciki. Lokacin da aka kira su, ana kiran su da "PCMs" Membobin Haɗin Kai.
Ana sa ran membobin da aka baiwa sunan Prospective Corp za su je asalin jihohin da aka tura su don yin hidimar, inda kuma za su idasa rajista da kuma motsa jiki a sansanin, wanda shine kashi na farko-(motsa jikin) na fara karbar horo a shekarar da za suyi hidimar.
Lokacin “wayar da kai” kusan makonni uku ne kuma ana yinsa a cikin “sansanin” da aka keɓe daga dangi da abokai. Akwai sansanonin a jihohi 36 na tarayya Najeriya.[5] A cikin makon farko da ake wayar musu da kai a mabanbanta sansanonin, ana rantsar da PCMs daga nan a ayyana su a matsayin membobin Corps. Hakanan akwai "bikin na gama karbar horo" daga nan a ƙarshen bayan shafe makonni ukkun da ake wayar musu da kai, ana tura membobin ƙungiyar zuwa wurin aikinsu na farko (PPA). Ana sa ran za su yi aiki a matsayin ma'aikata na cikakken lokaci a wuraren da aka tura su na farko-(PPA), sai dai ranar aiki guda ɗaya aka ware don aiwatar da aiki na ci gaban al'umma wanda aka fi sani da CDS. Bayan watanni goma sha ɗaya a PPA ɗin su, membobin ƙungiyar suna ba da izinin hutu na wata ɗaya kafin bikin ƙarewar hidimar na ƙarshe, inda za a ba su satifiket na shaidar kammalawa.[6]
Don samun cancantar shiga cikin masu yinhidimar shekara ɗaya ta tilas, wanda ya kammala karatun dole ne ya kasance ɗan ƙasa ko bai wuce shekaru 30 ba bayan kammala karatunsa, in ba haka ba za a ba shi (Certificate of Exemption), wanda kuma yayi daidai da takardar shaidar sallamar NYSC. Wanda ya gama karatu kafin ya shekara 30 amma ya tsallake shekarar hidimar zai ci gaba da cancanta tunda lokacin da ya kammala karatunsa bai cika shekara 30 da haihuwa ba. NYSC ya zama tilas ta yadda waɗanda suka kammala karatunsu a kasar nan ba za su iya neman a kebe su da kansu sai dai idan sun kasance nakasassu, sun yi aikin soja sama da shekara ɗaya ko kuma sun haura 30 a lokacin da suka kammala. Masu digiri na ɗan lokaci (CEP) ana keɓe su tunda ba a ba su damar yin hidimar ba.[7]
Ya kamata membobin ƙungiyar masu neman yin hidimar su sami ingantaccen adireshin imel mai aiki da lambar wayar Najeriya (GSM) don yin rajista. Hakanan ana buƙatar lambar JAMB da lambar Admishan-(matric number/reg. number) su ga waɗanda suka kammala karatunsu na gida a Nijeriya. Waɗanda su kayi karatu a ƙasashen waje kuma su tabbatar da cewa an amince da cibiyoyin da sukayi karatunsu na kasashen wajen. Hakanan, idan sun yi karatu a ƙasashen da ba na turawa ba, ana sa ran za su fassara abinda ke cikin satifiket naharshen Ingilishi kafin su bayar da satifiket ɗin ga hukumar-(NYSC) domin tantancewa. Hakanan yana da mahimmanci a lura cewa ba a ba da izinin yin rajista ta hanyar wakilai ba saboda kowane ɗan takara za a buƙaci ya yi gwajin (biometric screening).[8]
Waɗanda suka kammala karatun digiri a Najeriya ba su cancanci yin aiki a cibiyoyin gwamnati (da mafi yawan wasu cibiyoyi masu zaman kansu ba) har sai sun kammala hidimar shekara guda ta tilas ko kuma sun sami abin da aka keɓe masu da ya dace da kamar sun yi aikin hidimar. Wadanda suka kammala karatun digirin da aka kebe daga hidimar sun haɗa da waɗanda suka haura shekaru talatin da haihuwa da waɗanda ke da lalurar naƙasa. A cikin shekarar hidima, membobin Corps za su iya samun sabbin ƙwarewa kuma su koyi al'adun jihar da suke aiki a ciki.
An lissafta manufofin shirin bautar ƙasa na ƙasa a cikin doka mai lamba 51 na 16 ga Yuni 1993 kamar haka:
Shirin ya fuskanci suka daga wani yanki mai yawa na ƙasar da kuma ƙorafe-ƙorafe daga jami'an Corps game da albashinsu.[9] An kashe wasu tsirarun matasa da ke gudanar da shirin NYSC a yankunan da aka tura su saboda rikicin addini, ƙabilanci ko na siyasa.[10][11]
Bayan matsalolin tsaro, da yawa, wasu Samfuri:Su suwa ? sun nuna shakku kan ci gaban da shirin ke da shi, kuma sun yi kira da a gudanar da tattaunawa a kan wannan batu.[12] Dole ne a ɗauki matakan riga-kafi don kauce wa faruwar tashin hankali a nan gaba. Dole ne a kiyaye mutunci da martabar shirin ta hanyar magance batutuwan da aka ambata. Kwanan nan, an yi kira da a soke hukumar NYSC. Honarabul Awaji-Inombek Abiante ne ya ɗauki nauyin wannan kudiri, inda ya lissafta rashin tsaro a ƙasar nan, da kashe-kashen da ake yi wa masu yi wa kasa hidima, da gazawar kamfanoni masu riƙe mambobin ƙungiyar bayan sun yi aiki saboda tabarbarewar tattalin arzikin ƙasa, wasu daga cikin dalilan da ya sa hukumar ta NYSC ya kamata a soke ta.[13] Wannan kira na soke NYSC ya ci karo da ra’ayoyi mabambanta. Yayin da wasu shugabannin da suka shude ke adawa da a soke shi saboda ribar da ya samu ya fi hasarar da ake samu, wasu ‘yan Najeriya na ganin shirin ya yi hasarar amfani da shi don haka ya kamata a yi watsi da shi don kaucewa jefa rayukan ‘yan Najeriya marasa laifi ga rashin tsaro da kuma damuwa na shekara guda da ba dole ba.[14][15]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.