Lagos–Ibadan Railway
From Wikipedia, the free encyclopedia
Titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan, layin dogo ne mai tsawon kilomita 157 tsakanin Legas da Ibadan, tare da faɗaɗa kusan kilomita 7 don shiga layin dogo zuwa tashar jirgin ruwa a Legas.
Lagos–Ibadan Railway | |
---|---|
railway line (en) | |
Bayanai | |
Farawa | 2021 |
Ƙasa | Najeriya |
Date of official opening (en) | 10 ga Yuni, 2021 |
Terminus location (en) | Jahar Ibadan da Lagos, |
State of use (en) | in use (en) |
Gini
A shekarar 2017, kamfanin gine-ginen na kasar Sin ya fara aiki a kan layin dogo biyu. Titin jirgin kasa daga Legas zuwa Ibadan na ɗaya daga cikin aikin sabunta layin dogo na Najeriya wanda zai haɗa Lagos zuwa Abuja sai Kano ta hanyar Minna da Kaduna wanda tsawonsa ya kai kilomita 1315.[1] Bangaren Legas-Ibadan shine kashi na biyu na aikin.
Sai dai, don samun saukin aikin, an raba bangaren aikin Legas-Ibadan zuwa kashi uku. Na farko, gina Ebute Meta zuwa tashar Iju Ishaga; Na biyu, tashar Agbado zuwa Abeokuta; daga karshe kuma, tashar Abeokuta zuwa Ibadan. Kudin aikin ya kai dala biliyan 1.6.[2]
Aiki
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya kaddamar da aikin a wurin bikin kaddamar da cikakken harkokin kasuwanci a ranar 10 ga watan Yuni 2021.[3]
Manazarta
Wikiwand - on
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.