From Wikipedia, the free encyclopedia
Kura jam'in ta shine kuraye kura wata dabba ce mai launin kasa-kasa ko kuma ratsi-ratsi mafarauciyar nama (abincinta) tana daga cikin dabbobin daji masu hatsarin gaske. Wasu suna ganin kamar kura bata iya farauto abincin ta, sai dai ba haka zancen yake ba. Kura tana daga cikin dabbobin daji masu cin nama Kuma Naman ko wane iri ne ba wai sai dan'uwanta dabbobi ba har mutane takan kashe ta ci naman su. Da kura da zaki da sauran dabbobi masu cin nama dukkan su, suna da hatsarin gaske. Ana kuma kiran kalan wadannan dabbobin da turanci (carnivorous) wato masu cin nama ko wane irine. Sai dai kuma ita kura tana da ban tsoro sannan itama tana da tsoro sosai, ga tsoro ga ban-tsoro sai dai wani abinda baku sani ba game da kura shine, kura tana da basira sosai. Kuraye suna yawo kusan garke-garke, daga biyu zuwa fiye da haka, sai dai wasu masana sun tabbatar da cewa garken kuraye mafi yawa da aka taɓa gani, shine wanda aka gan kuraye saba'in da biyu (72) a garke daya.[1][2][3][4][5]
Kura (dabba) | |
---|---|
Scientific classification | |
Class | mammal (en) |
Order | Carnivora (en) |
Superfamily | Herpestoidea (en) |
dangi | Hyaenidae Gray, 1821
|
Geographic distribution | |
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.