Sallar Idi Babba
From Wikipedia, the free encyclopedia
Sallar Layya, Babbar Sallah, Eid al-Adha (larabci-ar|عيد الأضحى|ʿīd al-ʾaḍḥā|lit da turanci Feast of the Sacrifice), kuma ana kiranta da "Sallar Yanka/Sallar yin layya", shi ne biki na biyu da musulmai ke gudanarwa a duk duniya a kowace shekara, dayan bikin shi ne (Karamar Sallah), ana ganin wannan babbar ta fi daraja a cikin biyun. Allah ta'ala, ya karrama Annabi Ibrahim/Abraham (A.S), bayan ya mika wuya a Gare shi a kan yarda da yanka dansa Annabi Ismail (A.S) domin bin umurnin da Allah Ya bukace shi ya yi. Amma kafin Annabi Ibrahim ya yanka dansa, sai Allah ya aiko da babban rago ya yanka, sanadiyar haka ne ake yin yanka kuma ake raba naman gida uku, kaso daya, sadaka ga mabukata, na biyu a Raba wa 'yan'uwa, na uku wanda ya yi layyar ya ci abinsa.
| |
Iri |
Islamic holidays (en) public holiday (en) |
---|---|
Rana | 10 Dhu al-Hijjah (en) |
Bisa | Binding of Isaac (en) |
A kalandar musulunci 'Islamic lunar calendar'. Ana so a musulunce ka canja hanya a Yayinda kake dawowa daga idi, watau a canza hanya daga wadda aka bi a wurin zuwa.