From Wikipedia, the free encyclopedia
A ranar 15 ga watan Afrilu, 2023, rikici ya ɓarke a fadin kasar Sudan, musamman a babban birnin ƙasar Khartoum da yankin Darfur, tsakanin ɓangarorin gwamnatin mulkin sojan kasar. Ya zuwa ranar 20 ga watan Afrilu, kusan mutane 330 ne aka kashe kuma kusan 3,200 suka jikkata.[1]
| ||||
| ||||
Iri |
attempted coup d'état (en) civil war (en) rikici | |||
---|---|---|---|---|
Bangare na | 2019 Sudanese transition to democracy (en) | |||
Kwanan watan | 2023 | |||
Wuri | Khartoum | |||
Ƙasa | Sudan | |||
Participant (en) | ||||
Adadin waɗanda suka rasu | 413 (a data de 22 ga Afirilu, 2023) | |||
Adadin waɗanda suka samu raunuka | 3,000 (a data de 19 ga Afirilu, 2023) | |||
Hanyar isar da saƙo | ||||
Has part(s) (en) | ||||
timeline of the 2023 Sudan conflict (en) Operation Raus aus Khartum (en) |
Faɗan dai ya fara ne da hare-haren da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka kai kan muhimman wuraren gwamnati. An kai hare-hare ta sama da manya-manyan bindigogi a duk fadin kasar ta Sudan ciki har da Khartoum babban birnin ƙasar. Ya zuwa ranar 15 ga watan Afrilu, 2023 Shugaban RSF Mohamed Hamdan Dagalo da shugaban Sudan Abdel Fattah al-Burhan sun yi iƙirarin cewa suna riƙe da muhimman wuraren gwamnati da suka haɗa da babban ofishin sojoji, fadar shugaban kasa, filin jirgin sama na Khartoum, ofishin babban hafsan soji da kuma hedkwatar Sudan TV ta Sudan.[2][3][4][5]
A Tarihin rikice-rikice a Sudan ya ƙunshi rikice-rikice na kabilanci, rikice-rikice na addini, da gasa kan albarkatun ƙasar. [6] [7] A cikin tarihin zamanin nan, yakin basasa guda biyu tsakanin gwamnatin tsakiya da yankunan kudancin kasar ya kashe mutane miliyan 1.5, kuma rikicin da ake ci gaba da yi a yankin yammacin Darfur ya yi sanadin raba mutane miliyan biyu da muhallansu tare da kashe sama da mutane 200,000. Tun bayan samun ‘yancin kai a shekarar 1956, Sudan ta yi juyin mulkin soja sama da goma sha biyar kuma sojoji ne ke mulki a mafi yawan wanzuwar wuraren jamhuriyar ƙasar, tare da ɗan kankanen lokaci na mulkin farar hula na majalisar dokoki.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.