Per mertesacker
From Wikipedia, the free encyclopedia
Per Mertesacker An haife shi (29 ga watan September, 1984) ya kasance mai bada horo wato koci na Kasar jamus, sannan kuma dan wasa ne wanda yake buga baya. Kuma yanzu haka mai bada horo ne ko kuma koci a karamar kungiya ta Arsenal.
Per mertesacker | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Hanover, 29 Satumba 1984 (39 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Jamus | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahaifi | Stefan Mertesacker | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Abokiyar zama | Ulrike Stange (en) (2013 - | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa |
centre-back (en) Mai buga baya | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 200 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Kyaututtuka | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm1851124 |
Mertesacker ya fara gudanar da rayuwar shi ta kwallo bayan ya samu ci gaba tun yana dan saurayi inda ya samu damar doka gasar Bundesliga a wata kungiya mai suna Hannover96, inda ya fara buga wasa a matsayin kwararren dan wasa a shekarar alif 2003. Yana doka wurin baya ne a matsayin wurin da yake bugawa. Dan wasa ne mai natsuwa da kuma tarbiya sosai a cikin fili. Dan wasan ya buga wasanni 31 a lig ba tare da an fiddashi ba. Bayan namijin kokarin da yayi ma kungiyar tashi ta Hannover96 da kuma bajintar da yayi a kasarsa wato Jamus inda ya kasance yana cikin jerin yan wasan da suka buga gasar kofin duniya wadda akayi a shekarar alif 2006 inda ya buga gasar yana dan shekara ashirin da daya 21. Yabar kungiyar ta Hannover96, inda ya doka wasanni har guda 74 a kungiyar a gasar lig, daga bisani kuma ya koma kungiyar kwallan kafa ta Werder Bremen akan jumillar kudi £5m. Zamaninshi a kungiyar Bremen din abun yabawa ne inda ya nuna jajircewa da kuma juriya ta hanyar tare farmaki da kuma sanya ma abokan wasanshi nutsuwa. Sakamakon hakan, ya samu babbar nasara a wannan kungiya inda ya samu nasarar lashe DFB Porkal tare da kungiyar tashi a shekarar alif 2009. Sannan kungitar ta kare a cikin masu tsere na cin kofin UEFA Cup.
Bayan yabo da karbuwa da dan wasan ya samu a gasar kofin duniya na shekarar 2010, dan wasan ya matsa gaba inda yaje gasar Premier league inda ya kulla yarjejeniya da kungiyar Arsenal da jumillar kudi £8m. A kungiyar Arsenal, dan wasan ya shiga cikin mutum 11 na farko inda ake ganin yayi sa'a da kuma saurin shiga saboda yanayin girma da kuma kwararrun yan wasa da kungiyar keda su. Dan wasan ya shiga cikin manyan masu tsaron gida a kungiyar da kuma duniya ma baki daya. Ana yaban dan wasan akan kwanciyar hankali da nutsuwa da yake da ita. Dan wasan ya samu kyakyawar alaka da abokin aikinsa wanda suke tsaron gida tare wato Laurent Koscielny inda suka samu jituwa a cikin fili idan suna doka wasa. Sun shafe shekaru tara suna wasa tare kuma sun samu nasarar lashe gasanni da dama tare inda suna lashe kofin karshe a shekarar 2014 wanda suka buga da kungiyar Aston villa. Inda suka lallasa kungiyar Aston villa din daci 4-0 yayin da dan wasan ya samu damar jefa kwallo a raga.
Dan wasan ya zama captain na kungiyar Arsenal din saboda cancantar da yake da ita ta fannoni da dama. Daga bisani kuma ya dinga samun rauni ya dinga yawan yin jinya akai akai wanda hakan ne yasa ya ajiye tamaula a shekarar 2018.