Muhuyi Magaji Rimin Gado
From Wikipedia, the free encyclopedia
From Wikipedia, the free encyclopedia
Muhuyi Magaji wani ɗan siyasa ne kuma ɗan gwagwarmaya mai rajin yaƙi da cin hanci da rashawa a jihar Kano da kare hakkin dan Adam.
Ka duba wannan shafin domin sanin yanda zaka gyara wannan mukalar Koyon rubuta mukala
Akwai yuwar admin ya goge wannan shafin matukar ba'a inganta ta ba. |
Al’ummar jihar Kano sun fara sanin sunan Muhuyi Magaji Rimin Gado, a cikin shekarar 2010 lokacin da ya gurfanar da gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Gwamna Malam Ibrahim Shekarau a gaban kuliya, bisa nuna ƙin amincewarsa da naɗin ƴan siyasa a matsayin kantomomin riƙo, wanda hakan ya saɓa da kuma doka.
Muhuyi Magaji ya shigar da ƙarar ne yana neman kotu ta yi fassara kan sashi na Hamsin da Takwas karamin sashi na daya wanda ya baiwa gwamna da majalisa damar nada shugabannin kananan hukumomi, wanda a cewar mai karar, ta ci karo da sashi na Bakwai karamin sashi na daya a kundin tsarin mulkin Nigeria na shekarar 1999.
Muhuyi Magaji ya yi nasara akan gwamnatin jihar Kano, inda mai shari’a Muhammad Sadi Mato ya umarci gwamnan jihar Kano da kwamishinan shari’a da su nada mutanen da za su riki ragamar kananan hukumomin jihar Kano 44 har zuwa lokacin da hukumar zaben jihar za ta iya gudanar da zabe nan da dan lokaci.Ya taɓa dakatar da rantsar da shugabannin ƙananan hukumomi na riƙo a jihar Kano bayan da ya kai ƙorafi kotu, lokacin dai da yake matsayin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar.
Bayan da Gwamna Rabi'u Musa Kwankwaso ya koma mulki a shekarar 2015, Muhuyi ya zama jami'in ƙaramar hukuma na farko da ya mayar da motar gwamnati, wanda hakan ya tilasta wa sauran shugabannin ƙananan hukumomi mayar da nasu.
Ya ce ya yi hakan ne don tsayawa a kan gaskiya. Sai dai hakan ya jawo masa matuƙar baƙin jini a wajen takwarorinsa a lokacin.
A lokacin gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau tsakanin 2003 zuwa shekarar 2011 yayin da Muhuyi yake matsayin mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Rimin Gado, ya taɓa kai ƙorafi ga hukumar EFCC ta ƙasa kan wasu kuɗaɗen ƙaramar hukumar da suka maƙale.
A lokacin da kuɗin suka fito yana riƙon shugabacin ƙaramar hukumar, kasancewar shugaban ƙaramar hukumar ya yi tafiya. Kuma nan take ne ya fara gudanar da wasu ayyukan cigaba da kuɗaɗen a ƙaramar hukumar, lamarin da ya ja babu shiri shugaban ƙaramar hukumar ya dawo daga wata tafiyar da ya yi.
Wannan abu ya jawo saɓani tsakaninsa da shugaban ƙaramar hukumar ta Rimin Gado. Lamarin nan ya fara fito da Muhuyi a idon al'umma a matsayin mai yaƙi da cin hanci da rashawa.
Ya kafa wata ƙungiya mai zaman kanta wacce ke yaƙi da cin hanci da rashawa, kuma bayan nan ne Gwamna Abdullahi Umar ganduje ya naɗa shi shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jihar Kano a shekarar 2016.
Shugabancin hukumar yaki da cin hanci da rashawa da karbar koke-koken al'umma
Bayan Abdullahi Umar Ganduje ya zama gwamnan jihar Kano a shekarar 2015, ya naɗa Muhuyi Magaji Rimin Gado a matsayin shugaban hukumar karbar korafi da yaƙi da karɓar rashawa ta jihar Kano. Wannan muƙami da ya samu ya sanya masu sharhi akan al’amuran yau da kullum su ke kallon an ajiye ƙwarya a gurbinta la’akari da yadda aka naɗa jarumi kuma marar tsoro, matashi mai zuciyar ƴaki da rashawa da cin hanci da ƙoƙarin ganin an kakkaɓe dukkanin wata rashawa.
A lokacin da yake shugabantar hukumar ya koma ya yi karatun shari'a inda ya zama lauya.
Lokuta da dama ya sha nanata cewa Ba za mu ragawa duk wanda mu ka samu da karɓa ko bayar da cin hanci ba Archived 2021-07-13 at the Wayback Machine
Wasu masu sharhi kan al'amuran yau da kullum sun ce Muhuyi ya matukar ɗaga darajar hukumar ta cin hanci da rashawa ta jihar Kano, har ta zama hukumar da jami'an gwamnati da attajirai da 'yan kasuwa da sarakai suke tsoronta.
A lokacin da yake riƙe da wannan muƙami ya janyo ce-ce-ku-ce sosai inda ya dinga rigima da ɓangarori daban-daban.
Ya yi rigima da ma'ikatan kotu, ya binciki alƙalai, ya binciki manya-manyan ƴan siyasa, ya binciki Masarautar Kano Archived 2021-07-13 at the Wayback Machine har sau biyu duk kan zargin almundahana da ɓarnata kudaɗen gwamnati.
Sai dai wasu na yi masa zargin cewa ana amfani da shi don cimma wasu burikan siyasa, zargin da ya sha musantawa inda yake cewa yana aikinsa tsakaninsa da Allah.
Aranar 5 ga watan Yuli na 2021, majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Barista Muhyi Magaji Rimin Gado saboda kin karbar sabon akantan da Akanta Janar na Jihar Kano ya tura wa hukumar. Amma sai dai wasu majiyoyin sun bayyana babban dalilin dakatar da Muhuyi Magaji Rimin Gadon Archived 2021-07-14 at the Wayback Machine duk kuwa da cewa a nata bangaren majalisar jihar Kano wacce ta sanar da dakatarwar, ta ce, daukar matakin ya biyo bayan kin yin ladabi ga ofishin babban akantan jihar, ta hanyar kin amincewa da wani ma'aikaci da aka turawa hukumar yakin da cin hancin a matsayin babban akanta mai kirga lisaafi, daga bisani ,ma har shi Muhyi Magajin ya rubutawa akantan nadin takardar cewa An ki karbarka kuma ka kama gabanka'
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.