From Wikipedia, the free encyclopedia
Mohamed Salah Hamed Mahrous Ghaly (a Larabcin Misira محمد صلاح حامد محروس غالي) , an haifeshi a (15) ga watan yuni (1992), kwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Masar ne wanda yake buga wasa a gasar zakarun Turai da ƙungiyar Liverpool F.C. kuma yana bugawa a tawagar yan ƙwallon ƙasar Masar.
Muhammad Salah | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | محمد صلاح حامد محروس غالي | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Nagrig (en) , 15 ga Yuni, 1992 (32 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Misra | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harshen uwa | Larabci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Ƴan uwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Abokiyar zama | Magy Mohammed Sadek (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna |
Larabci Turanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa |
wing half (en) Ataka winger (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 11 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 71 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 175 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Kyaututtuka |
gani
| ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Imani | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Addini | Musulmi | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm7895524 |
Salah ya fara ne daga buga ƙwallon sa na kwararru a ƙungiyar sa ta gida El'Makawloon a gasar kwararru ta ƙasar Masar (2011),daganan kuma sai ya wuce ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Besel.A ƙasar Suwizalan, Salah ya samu nasarori da dama kamar (SAFP Golden Player award). Daga nan kuma Salah ya shiga ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea F.C akan kwantaragin £11 milyan na yuro a shekarar 2014.Daga nan kuma sai Salah ya sauya sheka da ƙungiyar dake wasanta SERIE 'A' wato Fiorentina a kan kwantaragin £15 milyan na yuro.
Bayan nasarorin da ya samu a Rome Salah daga karshe ya koma ƙungiyar da yake taka leda a yanzu ta Liverpool F.C dake ƙasar Ingila akan kwantaragin yuro na miliyan £36.9,a shekarar 2017.[1]
Salah a matsayin matashin ɗan ƙwallo a ƙungiyar El Makawloon. Sai ya shiga ƙungiyar kwararru ta ƙasar sa Masar.[2]
Salah ya kafa tarihi sosai a ƙungiyar Besel lokacin da yake buga masu wasa. Kamar a wasan da kungiyar sa ta buga filin wasa na Stadion Rankhof, Salah ya buga zagaye na biyun wasanne kawai amma saida yasamu damar zura kwallaye biyu a raga.[3]
A ranar 23 ga watan Janairu 2014 ne ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Chelsea ta fitar da sanarwar fara yarjejeniya da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Besel kan yiwuwar komar salah kungiyar a kan kwantaragin yuro miliyan £11. A ranar 26 ga Janairu na 2014 ne kuma dai Chelsea ta sake fitar da sanarwar kammala yarjejeniyar ta su inda Salah yazama dan kasar Masar na farko da zai taka leda a Stamford Bridge. A ranr 8 ga Janairun na 2014 ne kuma Salah ya fara nuna bajintar sa a wasan ƙungiyar sa ta Chelsea da kuma ta Newcastle. Ranar 22 ga Maris 2014 Salah yaci ƙwallon sa ta farko a wasan Chelsea da Arsenal.[4]
Ranar 2 ga watan fabrairu na shekarar 2015 Salah yabar kungir kwallon kafa ta Chelsea zuwa kungiyar kwallon kafa ta Fiorentina a matsayin bashi.
Ranar 6 ga watan Augusta shekarar 2015 Salah ya sake komawa ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Roma a matsayin bashi.[5]
A ranar 22 ga watan yuni 2017 ne Salah ya sauya sheka Zuwa ƙungiyar sa ta liverpool akan kwantargin yuro miliyan £42.[6]
Salah ya fara buga wasa ne a kungiyoyin kwallo na matasa na cikin gida. Salah yakan yi rashin makaranta don yin tafiyar awa 3 don motsa jiki. [7] Dole ne a ba Salah abinci na musamman da kuma shirin horo saboda rashin cikar tsokoki saboda karancin shekarunsa.
Ko da yake yana samun lokacin wasa akai-akai, Salah ya yi nasarar cin kwallaye da dama.
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.