![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/0c/Real_Valladolid_-_FC_Barcelona%252C_2018-08-25_%252879%2529_%2528cropped%2529.jpg/640px-Real_Valladolid_-_FC_Barcelona%252C_2018-08-25_%252879%2529_%2528cropped%2529.jpg&w=640&q=50)
Marc-André ter Stegen
From Wikipedia, the free encyclopedia
Marc-André ter Stegen (an haife shi 30 ga watan Afrilu shekara ta 1992) ƙwararren ɗan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Jamus wanda ke a matsayin mai tsaron gida a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Barcelona da kuma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta kasar Jamus . An ɗauke shi a dan wasa mai matukar farin jini a idon mutane lokacin da yake matashi, tun daga lokacin ya nuna kansa a matsayin daya daga cikin masu tsaron gida mafi kyau da juriya a kwallon kafa na duniya. An san shi da jujjuyawar sa, wucewa, da iya wasan tsaron gida, sau da yawa ana yi masa laƙabi da bangon Berlin saboda abubuwan da yake yi da kuma ikon sarrafa ƙwallon a matsayin mai tsaron gida[1].
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/b/ba/Bar%C3%A7a_-_Napoli_-_20140806_-_Marc-Andr%C3%A9_ter_Stegen_1.jpg/640px-Bar%C3%A7a_-_Napoli_-_20140806_-_Marc-Andr%C3%A9_ter_Stegen_1.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/5/54/Marc-Andr%C3%A9_ter_Stegen_%28FC_Barcelona%29%2C_Mattias_Ekstr%C3%B6m_%28EKS%29_%2820910648614%29_%28cropped%29.jpg/640px-Marc-Andr%C3%A9_ter_Stegen_%28FC_Barcelona%29%2C_Mattias_Ekstr%C3%B6m_%28EKS%29_%2820910648614%29_%28cropped%29.jpg)
![]() | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
![]() | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa |
Mönchengladbach (en) ![]() | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Jamus | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Jamusanci | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai tsaran raga | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Lamban wasa | 1 | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 85 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 187 cm | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
IMDb | nm4970127 |
Bayan yayi shekaru huɗu a Bundesliga tare da kungiyar Borussia Mönchengladbach, ya buga wasanni 108, bayan nan kuma sai ya koma Barcelona kan Yuro miliyan 12 a shekarar 2014. Ya lashe kofuna uku a kakar wasa ta farko a Spain, inda ya buga wa Barcelona wasa a Copa del Rey da kuma gasar zakarun Turai ta UEFA .
Ter Stegen ya wakilci kasar Jamus a matakai na matasa da yawa kuma ya fara buga wasansa na farko a duniya a shekara ta 2012. Ya kasance cikin tawagar Jamus da suka kai wasan kusa da na ƙarshe na UEFA Euro 2016 kuma ya lashe gasar cin kofin zakarun nahiyoyin duniya na 2017, kuma ya kasance memba a bangaren Jamus da suka halarci gasar cin kofin duniya ta FIFA 2018 [2].