![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/01/Reuven_Rivlin_with_Martin_Luther_King_III%252C_Pnina_Tamano-Shata%252C_Idan_Raichel_and_Anat_Saragusti.jpg/640px-Reuven_Rivlin_with_Martin_Luther_King_III%252C_Pnina_Tamano-Shata%252C_Idan_Raichel_and_Anat_Saragusti.jpg&w=640&q=50)
Mamman Shata
mawakin gargajiya a kasar Hausa Najeriya / From Wikipedia, the free encyclopedia
Alhaji Mamman ShataMamman Shata (Taimako·bayani), ya kuma rasu a shekara ta alif dari tara da chasa'in da takwas (1998), yana da shekara fiye da 70 a lokacin da ya bar duniya (rasu). Mamman Shata yana daya daga cikin Manyan mawakan gargajiyar da aka fi sani a kasashen Hausa da ma Afirka, kai har ma da duniya baki daya. Ya kasance mashahurin Mawaki, domin a fagen wakarsa ya shahara, Kasancewarsa a cikin wakar ba abin da ba zai iya yi wa waka ba idan ya ga dama.
![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Katsina, 1923 |
ƙasa | Najeriya |
Mutuwa | Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, 9 ga Yuni, 1999 |
Karatu | |
Makaranta | Makarantun Musulunci da Rassansu |
Harsuna | Hausa |
Sana'a | |
Artistic movement |
griot music (en) ![]() |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/01/Reuven_Rivlin_with_Martin_Luther_King_III%2C_Pnina_Tamano-Shata%2C_Idan_Raichel_and_Anat_Saragusti.jpg/640px-Reuven_Rivlin_with_Martin_Luther_King_III%2C_Pnina_Tamano-Shata%2C_Idan_Raichel_and_Anat_Saragusti.jpg)
" 'Yan Arewa Ku Bar Barci " na daya daga cikin wakokinsa.
Shata: 'Yan Arewa Ku Bar Barci, Najeriyarmu Akwai Dadi 'Yan Arewa a bar barci, Najeriyarmu akwai dadi. To!
'Yan Amshi: A a, 'Yan Arewa, a bar barci, Najeriyarmu, akwai dadi.
Shata: Kasar Afruka, bakar fata, Kasar Afruka, bakar fata, In ka yi yawo ciki nata. Duk ba kaman Najeriya, gidan dadi, Najeriya kasar farin jini, Najeriya ce gidan dadi, Balle Arewa uwar dadi. To!
'Yan Amshi: A a, 'Yan Arewa a bar barci, Najeriyarmu, akwai dadi.