![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/6/6c/Declaration_of_the_Rights_of_Man_and_of_the_Citizen_in_1789.jpg/640px-Declaration_of_the_Rights_of_Man_and_of_the_Citizen_in_1789.jpg&w=640&q=50)
Haƙƙoƙin ɗan'adam
From Wikipedia, the free encyclopedia
Hakkokin ɗan'adam, kyawawan ɗabi'u ne ko hanyoyin tafiyar da rayuwa na yau da kullum.[1] Shi ɗan'adam na da wasu kafaffun ɗabi'u, sannan kuma akan basu kariya ako da yaushe a matsayin haƙƙoƙin doka dana ɗabi'a a ƙarƙashin dokokin ƙasa da na duniya.[2] Ana ɗaukansu a matsayin haƙƙokin da ba'a iya tauye su,[3] tsararrun haƙƙoƙi ne "wanda kowanne mutum ke da haƙƙi akansu, badan komai ba sai don kasancewar ɗan'adam"[4] kuma "kowanne mutum yana da haƙƙi akansu",[5] ba tare da duba ga shekarun sa, jinsin sa, ƙasar sa ta asali, wurin zama, harshe, addini, ƙabila, ko kuma kowane irin babbanci ba.[3] Ana iya wanzar da su a ko ina a kuma ko da yaushe a zaman haƙƙi na duniya baki daya,[1] kuma yana daga ciki haƙƙoƙin ɗan'adam rashin nuna bambanci akan cewa dukkannin mutane daya suke.[3] Ana ɗaukar su a matsayin tausayin juna da kuma dokoki na shari'a[6] da kuma sanya wajabci akan kowane mutum da ya daraja wadannan Haƙƙoƙin na sauran mutane,[1][3] kuma ya amince gabaki daya akan ba za'a kore waɗannan haƙƙoƙi ba face idan akwai wasu dalilai na tsari.[7]
![]() | |
---|---|
convention (en) ![]() | |
![]() | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na |
Haƙƙoƙi da convention (en) ![]() |
Bangare na |
international law (en) ![]() |
Foundational text (en) ![]() | Gamayyar Sanarwa na Yancin Dan'adam |
Hashtag (en) ![]() | StandUp4HumanRights |
Babban tsarin rubutu | Yarjejeniyar Turai kan Haƙƙin Dan Adam |
Gudanarwan | Mai kare ƴancin ɗan'adam |
Personal library at (en) ![]() |
University of Minnesota Libraries (en) ![]() |
WordLift URL (en) ![]() | http://data.thenextweb.com/tnw/entity/human_rights |
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/e/ee/Magna_Carta_%28British_Library_Cotton_MS_Augustus_II.106%29.jpg/640px-Magna_Carta_%28British_Library_Cotton_MS_Augustus_II.106%29.jpg)
Koyarwar Haƙƙin ɗan'adam yayi fice a tsakanin Ƙungiyoyin shari'a na ƙasa da ƙasa. Matakai da Jihohi da kuma Ƙungiyoyin da ba na gwamnati ba (NGO's) ne suka kafa tushen dokokin al'umma a duk fadin duniya. Ra'ayoyin Haƙƙin ɗan'adam sun bayyana cewa idan Ƙungiyoyin al'umma zasu zauna su tattauna akan matakan zaman lafiya ga al'ummomin duniya, to wannan za'a iya cewa ya zamo Ƙarshen kyawawan dabi'u na gama gari, Waɗannan su ne haƙƙokin ɗan'adam". Mayan hujjojin kare Haƙƙin ɗan'adam sun saɓawa koyarwa da dama na addinai, kuma suna jayayya akan abubuwan da dokokin suka ƙunsa, tsarinta da kuma sharuddanta har zuwa yau. Anyi jayayya sosai akan asalin ma'anar kalmar haƙƙi, kuma ya zamo darasi na jayayya wanda baya karewa,[8] a yayinda anyi amanna akan cewa haƙƙokin ɗan'adam sun ƙunshi Haƙƙoƙi da dama, kamar adalci a shari'a, kare ɗan'adam daga zama bawa, da kuma yancin faɗin albarkacin baki,[9] da kuma haƙƙokin samun ingantaccen Ilimi, akwai saɓani akan wanne daga cikin Waɗannan haƙƙoƙi ne zasu zamo daga cikin jigon haƙƙokin ɗan'adam ;[1] wasu manazarta sun ayyana cewa ya kamata aƙalla haƙƙin ɗan'adam ya zamo ƙaramin doka don hana mummunan cin zarafi, a yayinda wasu kuma suke gani cewa shine kololuwar sharaɗi.[1][10] Har ila yau, anyi jayayya cewa haƙƙin ɗan'adam doka ne daga Ubangiji; duk da cewa anyi suka ga wannan ra'ayi sosai.[11]
Muhimman ra'ayoyin da suka janyo wannan cece-kuce na Haƙƙin ɗan'adam