From Wikipedia, the free encyclopedia
Baƙin Dutse (da larabci ٱلْحَجَرُ ٱلْأَسْوَد), "al-Ḥajaru al-Aswad") wani dutse ne da aka sanya shi a bangaren gabashin jikin Kaaba, ginin tarihi da aka Gina shi a tsakiyar Masallacin Harami a Mecca, Saudi Arabia. An sake sabunta ginin Kaaba ne, amatsayin ginin da yakasance tun daga zamanin annabi Adam da Hauwa.[1]
Baƙin Dutse | ||||
---|---|---|---|---|
dutse da heirloom (en) | ||||
Bayanai | ||||
Bangare na | Kaaba | |||
Suna a harshen gida | ٱلْحَجَرُ ٱلْأَسْوَد | |||
Ƙasa | Saudi Arebiya | |||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Saudi Arebiya | |||
Province of Saudi Arabia (en) | yankin Makka | |||
Tourist attraction (en) | Makkah |
Ansanya dutsen ne a Kaaba tun a gabanin musulunci, lokacin jahiliyya. Kamar yadda tarihin ya bayyana, dutsen ansanya shi ne a jikin bangon Kaaba da annabi Muhammad yayi a 605 CE, shekaru biyar kafin wahayin farko. Tun daga wannan lokaci an farfasata zuwa kanana kanana amma ayanzu an hade shi cikin tasgaron tagulla a Kaaba. Yadda ake ganinsa ayanzu shine wani tsagaggen dutse mai duhu, yayi silɓi saboda hannayen mahajjata dake taɓa shi koda yaushe. Musulunci an bayyana cewa dutsen ya fado ne daga aljanna amatsayin kwatance ga Adam da Hauwa dan su gina gun bauta. Kuma wasu sun bayyana shi amatsayin dutse ne ya fado daga sama, wanda ake kira da meteorite.
Mahajjata na kewaye dakin Kaaba amatsayin ɗawafi bauta, mafi yawan mahajjatan kanyi ƙoƙarin tsayawa dan sunbantan baƙin dutsen, da danganta sunbantar amatsayin sunnar da annabi Muhammad yayi wa dutsen lokacin rayuwarsa.[2][3] Musulmai basu bautawa baƙin dutsen.[4][5]
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.