Báb
From Wikipedia, the free encyclopedia
Sayyid Alí Muḥammad (20 Oktoba1819 - 9 Yuli 1850) wani ɗan kasuwa ne daga Shíráz, Iran wanda ya fara wani tsari na Shia mai suna Bábism. Bayan ya fara addinin, ya canza sunan sa zuwa Báb. Mutanen da suka yi imani da Báb ana kiran su Bábís, kuma sun yi imani cewa Bab annabi ne . Bábís kuma yi imani da cewa Bab ne Qá'im cewa Shi'as sunyi imani zai zo a nan gaba.
Báb | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | عَلی مُحَمَّد شیرَازی |
Haihuwa | Shiraz, 20 Oktoba 1819 |
ƙasa |
Daular Qajar Iran |
Mutuwa | Tabriz, 9 ga Yuli, 1850 |
Makwanci | Shrine of the Báb (en) |
Yanayin mutuwa | hukuncin kisa (gunshot wound (en) ) |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Khadíjih-Bagum (en) (1842 - 1850) |
Sana'a | |
Sana'a | religious figure (en) , Mai da'awa, Manifestation of God (en) da Ɗan kasuwa |
Imani | |
Addini | Bábi |
Báb ya rubuta ɗaruruwan wasiƙu da littattafai yana koyar da addinin shi kuma menene dokokin addinin sa. Sabbin dokokin na Bab sun maye gurbin " shari'ar Sharia " ko dokokin musulmai ga mabiyan a. Bábism ya zama babba; sama da mutane dubu goma suka yi imani da Báb. Malaman Shi'a, ko shugabannin Musulunci a Iran sun ƙi jinin Bab ɗin kuma suna ƙoƙarin cutar da mutanen da ke bin addininsa. A cikin shekarar dubu ɗaya da ɗari takwas da hamsin 1850 wasu ingan bindiga suka harbi Bab a Tabríz, Iran .
Báb din yana da wasu sunaye, misali "Maɓallin Farko" da "Maɓallin Bayán"
Bab ɗin ya faɗawa kowa cewa wani annabin da ya fi karfi kuma ya fi iko yana nan tafe. Mutanen da ke bin addinin Ba'a'í sun yi imani cewa Bab yana magana ne game da Bahá'u'lláh, wanda ya fara addinin Baha'i