From Wikipedia, the free encyclopedia
Attica ( Greek: Περιφέρεια Αττικής , [periˈferi.a atiˈcis] ) yanki ne na siyasa ne a Girka, wanda ya mamaye duk yankin manyan biranen Athens, babban birnin ƙasar kuma birni mafi girma. Yankin yana hade da tsohuwar gundumar Attica ta Tsakiyar Girka. Yankin ta ƙunshi yanki mafi girma fiye da yankin tarihi na Attica.
Atika | |||||
---|---|---|---|---|---|
Περιφέρεια Αττικής (el) | |||||
| |||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Ƴantacciyar ƙasa | Greek | ||||
Government agency (en) | Decentralized Administration of Attica (en) | ||||
Babban birni | Athens | ||||
Yawan mutane | |||||
Faɗi | 3,814,064 (2021) | ||||
• Yawan mutane | 1,001.57 mazaunan/km² | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Decentralized Administration of Attica (en) | ||||
Yawan fili | 3,808.1 km² | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Attica Prefecture (en) | ||||
1987 2011: Kallikratis Plan (en) | |||||
Tsarin Siyasa | |||||
• Gwamna | Giorgios Patoulis (en) (2019) | ||||
Bayanan Tuntuɓa | |||||
Kasancewa a yanki na lokaci | |||||
Lamba ta ISO 3166-2 | GR-I | ||||
NUTS code | EL30 | ||||
Wasu abun | |||||
| |||||
Yanar gizo | patt.gov.gr | ||||
Attica na nan a gefen gabas ta tsakiyar Kasar Girka, tana da fadin murabba'in kilomita 3,808. Bugu da ƙari, Athens, na ƙarkashin yankinta, biranen Elefsina, Megara, Laurium, da Marathon, da kuma wani karamin yanki na Peloponnese Peninsula da tsibiran Salamis, Aegina, Angistri, Poros, Hydra, Spetses, Kythira . da Antikythera . Kimanin mutane 3,800,000 ke zaune a yankin, wanda sama da kashi 95% mazauna yankin babban birnin Athens ne. A cikin shakara ta 2019, Attica tana da HDI na 0.912, mafi girma a Girka.
An kafa yankin a yayin sake fasalin yankuna na 1987, kuma har zuwa 2010 yankin ta ƙunshi larduna 4 na Athens, Gabashin Attica, Piraeus da West Attica .
Tare da shirin Kallikratis na shekara ta 2010, an sake matsayin yankin da aka gaba daya sake fasalin da kuma mika. Tun daga 1 ga Janairu 2011, yankin yana wakiltar ƙaramar hukuma mataki na biyu. Duk da yake ana kula da shi daga Hukumar Gudanarwa ta Attica, yanzu ita ce hukuma mai zaman kanta mai cin gashin kanta tare da iko da kasafin kuɗi mai kama da tsoffin lardunan.
An raba yankin zuwa yankuna guda takwas:
Yankin Attica ta ƙunshi gundumomi takwas na zaɓe : Athens A, Athens B1, Athens B2, Athens B3, Piraeus A, Piraeus B, Attica Gabas da Yammacin Attica .
Seamless Wikipedia browsing. On steroids.
Every time you click a link to Wikipedia, Wiktionary or Wikiquote in your browser's search results, it will show the modern Wikiwand interface.
Wikiwand extension is a five stars, simple, with minimum permission required to keep your browsing private, safe and transparent.