![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/4/42/Arjen_Robben_v_Shakhtar_2015_%2528cropped%2529.jpg/640px-Arjen_Robben_v_Shakhtar_2015_%2528cropped%2529.jpg&w=640&q=50)
Arjen Robben
From Wikipedia, the free encyclopedia
Arjen Robben ( Dutch pronunciation: [ˈɑrjən ˈrɔbə(n)] ( </img> ; an haife shi ne a ranar 23 ga watan Janairu a shekara ta alif ɗari tara da tamanin da hudu1984A.c) tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne wanda yake taka leda a matsayin winger wanda ya iya cin nesa ana mai laqabi ne da mai lauje . An san shi da basirar iya yanke yanke, gudun, sarrafa ƙwallo da harbi mai tsayi. Ana daukar Robben a matsayin daya daga cikin fitattun 'yan wasa na zamaninsa kuma ana yaba masa a matsayin daya daga cikin mafi kyawun wiwi a duniya a lokacinsa.
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/4/42/Arjen_Robben_v_Shakhtar_2015_%28cropped%29.jpg/320px-Arjen_Robben_v_Shakhtar_2015_%28cropped%29.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/1/14/Arjen_Robben_2444.jpg/640px-Arjen_Robben_2444.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/8/8c/Arjen_Robben_2649.jpg/640px-Arjen_Robben_2649.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/f/f6/Arjen_Robben_Training_2016-11_FC_Bayern_Muenchen-3.jpg/640px-Arjen_Robben_Training_2016-11_FC_Bayern_Muenchen-3.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/1/18/Bernadine_und_Arjen_Robben_2656.jpg/640px-Bernadine_und_Arjen_Robben_2656.jpg)
![Thumb image](http://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/9/93/Arjen_Robben_travel.jpg/640px-Arjen_Robben_travel.jpg)
Robben ya fara yin fice dasaninshi a tare da Groningen, wanda shi ne gwarzon shekara ta dubu biyunxuwa dubu biyu da daya a qasar nezaland na shekarar, 2000 zuwa 20001 Eredivisie kakar. Shekaru biyu bayan haka ya rattaba hannu kan PSV aqasar nezaland din, inda ya zama matashin dan wasa na shekara na qasar Netherlands kuma ya lashe taken Eredivisie . A kakar wasa ta gaba manyan kungiyoyi ne suka bi sa hannun kwamtiragin matashin dan wasan a lokaci Robben, kuma bayan tsawaita tattaunawar canja wuri, ya koma dake nan birnin landan a qasar burtaniya Chelsea a shekara ta, 2004. An jinkirta wasan farko na Robben na Chelsea ta hanyar rauni, amma bayan dawowarsa cikin koshin lafiya, ya taimaka wa Chelsea ta kawo kofunan gasar Premier biyu a jere, kuma shi ne Gwarzon dan wasan Premier a watan Nuwamba a shekarar dubu biyu da biyar, 2005. Bayan kakar wasa ta uku a Ingila wanda ya samu rauni, Robben ya kulla yarjejeniya da Real Madrid tana qasar sipaniya a kan kudi Yuro miliyan talatin da biyar 35.
A watan Agustan shekarar dubu biyu da tara 2009, Robben ya koma Bayern Munich akan farashin kusan Yuro miliyan ashrin da biyar. A kakarsa ta farko a Munich a qasar jamus, Bayern ta lashe gasar lig, wanda Robben ya lashe a karo na biyar cikin shekaru takwas. Robben ya zira kwallayen nasara a gasar cin kofin zakarun Turai ta inda uska yasamu gasar cin wasan a shekarar, 2013 na karshe, ana kiransa shi ga Squad of the Season. A cikin shekara ta, 2014, an ba shi suna zuwa FIFPro World XI da UEFA Team of the Year, da kuma matsayi na hudu a cikin gasar dan yan qwallo da sukafi kowane a shekrai Ballon d'Or . A Jamus, ya lashe kofuna 20, gami da taken Bundesliga takwas da DFB Pokals biyar. A cikin dogon lokaci da ya yi a Bayern, Robben kuma an san shi da kyakkyawar haɗin gwiwa tare da ɗan wasan winger Franck Ribery - tare ana kiran su da ƙauna da sunan barkwanci . A ranar 15 ga watan Yuli a shekara ta, 2021, Robben ya ba da sanarwar yin ritaya daga ƙwallon ƙafa.
Robben ya fara ne a gasar cin kofin duniya ta FIFA a shekarai dubu biyu da goma, 2010, wanda Nezaland din ta sha kashi a hannun spaniya daci daya mai ban haushi. Ya bayyana a gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekarar, 2004 da 2008 da 2012 da kuma gasar cin kofin duniya ta FIFA na shekarar, 2006 da 2010 da 2014 . A karshen, ya lashe Bronze Ball kuma an kira shi ga All-Star Team .