![cover image](https://wikiwandv2-19431.kxcdn.com/_next/image?url=https://upload.wikimedia.org/wikipedia/commons/thumb/0/00/Nok_Kultur%252C_Nigeria._Fragment_eines_Gef%25C3%25A4%25C3%259Fes_mit_mehreren_Figuren_im_Halbrelief..jpg/640px-Nok_Kultur%252C_Nigeria._Fragment_eines_Gef%25C3%25A4%25C3%259Fes_mit_mehreren_Figuren_im_Halbrelief..jpg&w=640&q=50)
Al'adar Nok
From Wikipedia, the free encyclopedia
Al'adar Nok, da turanci Nok culture takasance wata al'umma ce da suka rayu tun a Zamanin Karfe, kuma ayyukansu da kayayyakinsu wadanda akasamu a yankin ake dangantasu da sunan mutanen kauyen Ham dake garin Nok din jihar Kadunan Nijeriya, wanda ananne aka samu shahararrun sarrafe-sarrafan ayyukan su na farko a shekara ta 1928. Al'adun Nok dai ansamesu ne a arewacin Najeriya tun a 1500 BC [1] kuma sun lalace ne a shekarar 500 AD batare da wani abu ba, amma dai sun sauki kusan shekaru 2,000 kafin lalacewarsu.[2]
![]() | |||||
---|---|---|---|---|---|
archaeological culture (en) ![]() ![]() | |||||
![]() | |||||
Bayanai | |||||
Farawa | 15 century "BCE" | ||||
Suna saboda | Nok | ||||
Ƙasa | Najeriya | ||||
Lokacin gamawa | 1 "BCE" | ||||
Time period (en) ![]() |
Iron Age (en) ![]() ![]() | ||||
Dissolved, abolished or demolished date (en) ![]() | 1 "BCE" | ||||
Wuri | |||||
|
Amfani da karafa, da kyere-kyeren kayayyaki da kira anfara su a garin Nok tun kusan 550 BC ko kafin nan ma, Bayanai da aka samu musamman cikin amfani da kuma harsunan su ya nuna cewar anfara sune tun a kafin shekarar 1000 BC.[3][4] ayyukan dasuka shafi kimiyya sun faro ne a shekarata 2005, kawai Dan ayi binciken yankunan da akwai birne birne a garin, da kuma dan fahimtar sarrafe sarrafan aladun mutanen musamman na zamanin karafa.[5][6][7]