Zogale
From Wikipedia, the free encyclopedia
Zogale ko Zogala (Moringa oleifera) nau'ine a cikin nau'in ganye wanda kuma akan sarrafa shi wajan yin magani, miya kwado da sauransu. Zogale na iya girma ya kai tsayin bishiya, amma a ainihin tsarin "daga tsirrai na duniya" (ICBN), yawancin zogale ba bishiya ba ce.
Zogale | |
---|---|
Conservation status | |
Least Concern (en) (IUCN 3.1) | |
Scientific classification | |
Kingdom | Plantae |
Order | Brassicales (en) |
Dangi | Moringaceae (en) |
Genus | Moringa (en) |
jinsi | Moringa oleifera Lamarck, 1785
|
General information | |
Tsatso | ben oil (en) , Moringa oleifera extract (en) , Moringa oleifera fruit (en) da Moringa oleifera seed (en) |
Shi tushen zogale yana ɗaya daga cikin tsirran da Allah Ya yi wa albarka kasancewar bincike-binciken kimiyya ya tabbatar da cewa yana da amfani a fannoni da dama na inganta lafiyar Dan'adam. Zogale yana kuma kumshe da sinadaran dake warkar da cututtuka kamar ciwon suga, hawan jini, da kuma yawancin cututtukan da wasu irin kwayoyin halittu wadanda idon mutum baya iya ganinsu (in ba tare da na'urar kambama qananan halittu ba) suke sabbabawa. A saboda haka, kamar yadda yawancin jama'a suka sani, cin zogale da yin miyar sa da shan shayin shi, hadi da shan ruwan shi, cikin yardar Allah, zai yi sanadiyyar samun waraka daga cututtukan da aka ambata a sama, dama wasu wadanda ba a ambata ba. Zogale yana ƙara lafiyan jiki sosai, yana kuma daga cikin nau'in abincin da masu shekaru 40 zuwa sama ya kuma kamata su rika amfani da shi.