Abacha
Gari a Jihar Anambra / From Wikipedia, the free encyclopedia
Abacha birni ne, da ke a jihar Anambra a kudu maso gabashin Najeriya. Birnin ya yi iyaka da garuruwan Abatete, Nimo, Oraukwu da Eziowelle. Haka-zalika ya na ɗaya daga cikin al'ummomi goma da ke karamar hukumar Idemili North a jihar Anambra, sannan kuma ya na a cikin shiyyar Sanatan Anambra ta tsakiya. Al’ummarta na cikin al’ummomin da ke magana da harshen Igbo a yankin da ke gabashin Najeriya. Garin Abacha ya ƙunshi ƙauyuka biyar da hukuma ta tabbatar; Umudisi, Umuazu, Umuokpolonwu, Umuekpeli, da Ugwuma, tare da 'yan uwan Nogba da suke burin zama ƙauyen nasu. Kauyen Umuokpolonwu na Abacha yana da kauyuka biyu, wato: Umunneora da Umuaribo.